Matar Tinubu Ta Bayyana Babban Sirrin Farin Jinin Mijinta, Ta Ce Ba Kuɗi Bane Kamar Yadda Wasu Ke Zato

Matar Tinubu Ta Bayyana Babban Sirrin Farin Jinin Mijinta, Ta Ce Ba Kuɗi Bane Kamar Yadda Wasu Ke Zato

  • Misis Remi Tinubu, mai dakin dan takarar shugaban kasa na APC a zaben 2023 ta bayyana sirrin farin jinin mijinta
  • Remi ta ce Asiwaju mutum ne mai sakin hannu kuma yana da tausayi da jin kai hakan yasa mutane ke son shi amma ba don yana da kudi ba
  • Sanata na Legas ta bayyana cewa ko kwanaki biyu da suka gabata sai da ta roki kudi naira miliyan 2 daga wurin Misis Shettima, matar Kashim Shettima

FCT Abuja - Matar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Sanata Oluremi Tinubu, ta ce sirrin farin jin mjinta ba kudi bane amma yawan kyauta.

Ta bayyana hakan ne wurin wani taron jin ra'ayin mutane da aka yi a tare da mutane masu bukata da musamman a Abuja, ranar Alhamis, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugabancin Kasa Na 2023: Tinubu Ba Kudi Ya Ke Nema Ba, Hajiya Maryam Salihu

Remi Tinubu
Matar Tinubu Ta Bayyana Sirrin Mijinta, Ta Ce Ba Kuɗi Bane Kamar Yadda Wasu Ke Zato. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta ce abubuwa za su sauya idan aka zabi mijinta yayin da zai dora kan nasarorin Shugaba Muhammadu Buhari.

Ko jiya sai da na roki Shettima Naira miliyan 2, In Ji Remi Tinubu

Kalamanta:

"Sirrin Asiwaju ba kudi bane, akasin abin da mutane ke tunani, mutum ne mai tausayi kuma yana da kyauta. Ba abin da ba zai iya bada wa ba. Asiwaju yana rike kudi? Ba kasafai ba. Na tuna bayan ya gama gwamna, muna da wani ma'aikacinsa a gida, idan kana bukatar wani abu zai ce ka tafi ka same wane da wane, haka ya ke.
"Abin da mutane ke maka zato, Allah ya tabbatar. Idan sun ce yana da kudi, ina mamaki, Misis Shettima ta san cewa jiya na roke ta naira miliyan 2. Ina fada wa mutane ba don kudi bane, mutane suna zuwa ralli ne don yana basu kwarin gwiwa a wannan lokaci na wahala. Idan ba mu fatan gaba mai kyau, ba za mu iya cigaba da rayuwa ba."

Kara karanta wannan

Zabin Allah Na Bi: Bidiyon Soyayya Da Wata Kyakkyawar Mata Da Mijinta Mai Nakasa Ya Tsuma Zukata

Matsayin Najeriya yanzu tamkar mace mai nakuda ne, Remi Tinubu

Ta kwatanta halin da kasar ke ciki kamar mace da ke nakuda, tana mai cewa Najeriya na daf da haifar da alheri.

Ta yi kira ga al'ummar kasar su zabi tikitin musulmi da musulmi tunda yan hana ruwa gudu ba su bari dayan abin da aka zaba ya yi nasara ba.

Ta kara da cewa idan bayan shekaru hudu ba su gamsu ba suna iya zaben wata jam'iyyar daban.

Shehu Sani ya magantu kan jam'iyyar da ya dace gwamnonin da ke fushi da jam'iyyarsu su shiga

A wani rahoton, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, kwamared Shehu Sani ya shawarci gwamonin Najeriya da ke kai ruwa rana da shugabannin jam'iyyarsu su hakura su koma jam'iyyar Omoyele Sowore ta AAC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel