Shugabancin Kasa Na 2023: Tinubu Ba Kudi Ya Ke Nema Ba, Hajiya Maryam Salihu

Shugabancin Kasa Na 2023: Tinubu Ba Kudi Ya Ke Nema Ba, Hajiya Maryam Salihu

  • Wata jigo a jam'iyyar APC daga Arewa ta Tsakiya, ta bayyana cewa Tinubu ya na takara ne don ceto kasar nan daga halin da take ciki
  • Jigon ta kuma shaida cewa idan don kan sa ne ba zai fito takara ba, saboda ya na da kudin sa ba azurta kansa yazo yi ba
  • An yi kira da mata da matasa da su zubawa Tinubu ruwan kuri'a don kawo karshen matsalolin Najeriya

Dan takarar shugabancin kasa a inuwar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, yana takara ne don mayar da Najeriya kasar da kowa zaiji dadin ta, a cewar wata babbar jigon jam'iyyar APC (Arewa ta Tsakiya), Hajiya Maryam Salihu.

A cewar ta, Tinubu ba yana takara a zaben 25 ga Fabrairu domin azurta kan sa ba ne, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Roki Gwamnatin Dubai Ta Cirewa yan Najeriya Takunkumin Hana Shiga

Bola Tinubu
Shugabancin Kasa: Tinubu Ba Kudi Ya Ke Nema Ba, In Ji Jigon APC. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Tinubu yana da kudi, ba don neman arziki yasa ya ke son zama shugaban kasa ba, Hajiya Maryam Salihu

Ta bayyana haka ne a wani taron rabon tallafin kungiyar National Agenda for Greater Asiwaju, daya daga cikin daruruwan kungiyoyin goyon bayan Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce:

''Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mutum ne mai tsari, ba shi da son kai. Yana takara ne don tallafawa Najeriya ta zama abar alfahari ga mutanen kasar har ma da masu tasowa. Najeriya zata zauna lafiya a hannun Asiwaju; yana da kudi, yana kuma da tasiri. Ba kan sa yake wa takara ba don kowa yake.
''Idan ka kalli wanda ke tsagaye da shi, ba wai iya na kusa da shi ya ke tallafawa ba, tallafin sa ya zagaye ko ina a kasar nan. Irin wannan shugaban muke da bukata. Asiwaju mutum ne da yasan halin da duniya ke ciki, ba shi da son kai, ba bukatun kan sa yake dubawa ba. Idan don ta shine, ba na tunanin zai nemi shugabancin kasar nan.''

Kara karanta wannan

Buhari a Sokoto: Tinubu ya Matukar Fahimtar Matsalolin Najeriya, Ku Zabe Shi

Tun da farko, shugabar kungiyar NAGA kuma mataimakiyar darakta, kwamitin yakin neman zaben APC, Hajiya Hadiza Vatsa, ta bayyana cewa an shirya bayar da tallafin da nufin taya murna ga Tinubu da abokin takarar sa, Kashim Shettima.

Ta ce NAGA ta karfafa shirin ta a kokarin ganin sun cika alkawarin kuri'a miliyan 2.5 ga Tinubu.

A cewar ta, shirin bada tallafin hanya ce ta isar da sako ga yan Najeriya kan ingancin Tinubu a babban zabe mai zuwa.

Vatsa ta ce:

''Bani da shakka idan aka zabi Tinubu da Shettima ranar 25 ga Fabrairu, zaman lafiya zai mamaye Najeriya. Ba za a samu matsala ba. Idan babu zaman lafiya, komai ma babu. Zaman lafiya shine babban abun da muke bukata don bunkasa Najeriya.
''Tinubu cikakken mutum ne. Na fara tun daga tushe don nemawa Tinubu goyon baya. Duk matsalolin kasar nan sun zama tarihi idan aka zabi Asiwaju.

Kara karanta wannan

Iyorchia Ayu ya Kwabsa a Kano, Yace PDP ta Tafka Abun Kunya Yayin Kamfen din Atiku

''Ina kira ga mata da matasa da su fito kwan su da kwarkwata su kuma zabi Ahmed Tinubu a zaben watan Fabrairu.''

Gbajabiamila ya ce fallasa wadanda suka kirkiri karancin man fetur da sabbin takardun naira

A wani rahoton, Femi Gbajabiamila kakakin majalisar tarayyar Najeriya ya yi ikirarin cewa wasu masu 'neman hana ruwa gudu' ne suka kirkiri karancin man fetur da sabbin naira don dakile yiwuwar nasarar Bola Tinubu, dan takarar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel