Kyakkyawar Matar Aure Ta Nunawa Duniya Mijinta Mai Nakasa a Bidiyo Mai Daukar Hankali

Kyakkyawar Matar Aure Ta Nunawa Duniya Mijinta Mai Nakasa a Bidiyo Mai Daukar Hankali

  • Wata kyakkyawar mata wacce ta auri miji mai nakasa ta jinjina soyayyar da suke yi wa junansu
  • A wani hadadden bidiyo mai ratsa zuciya da ya yadu a TikTok, ta nuna irin soyayyar da take masa sannan ta bayyana dalilinta na auren shi
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun rubuta dadaddan zantukan soyayya da karfafa gwiwa ga ma'auratan wadanda suka haifi da daya tare

Wata kyakkyawar mata ta wallafa bidiyo mai daukar hankali tare da mijinta wanda ke da nakasa.

A cikin hadadden bidiyon, an gano su zaune kusa da junansu yayin da suke kallon kansu cike da shaukin so da kauna.

Mata da miji
Kyakkyawar Matar Aure Ta Nunawa Duniya Mijinta Mai Nakasa a Bidiyo Mai Daukar Hankali Hoto: @theclements2020
Asali: TikTok

Yayin da take wallafa bidiyon ta TikTok, matar mai cike da alfahari ta bayyana dalilinta na auren mutumin mai nakasa.

A cewarta, shine zabin Allah a gareta kuma bata son bijirewa hanyar da Allah ya daura ta a kai.

Kara karanta wannan

Kai Mummuna Ne: Budurwa Ta Kunyata Saurayi, Ta Ki Amincewa Ta Aure Shi, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce:

"Kana zaban abokin rayuwa bisa da taimakon Allah ba wai saboda abun da mutane za su ce ba."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@nadixmore ta ce:

"Wannan gaskiya ne abun da duniya ke tsammani ya sha bamban da fadar Allah kuma wannan ne dalilin da yasa soyayya da dama basa kaiwa ko'ina."

@lizzybebe7 ta ce:

"Irin wannan ne soyayyar da nake so amma abun takaici yana da matukar wahalar samu. Ina nufin duba wadannan martanonin abun haushi."

@kay_luv.0 ta yi martani:

"Mafi akasarin lokuta mutane basa tunani kan sauran jama'a baya ga kansu, basa yi kuma basa taba fahimtar irin aiki da kokarin da mutum ke yi a kansu."

@jabumm ta yi martani:

"Idan ka ga irin wannan soyayyar sai ka gaza hakuri har sai ka tambayi Ubangiji ni dankali ne ina mutumina. Wannan ya yi kyau."

Kara karanta wannan

Bidiyon Kyakkyawar Gurguwa Tana Tikar Rawa Da Kafa Daya Cike da Kwarewa Ya Ba Da Mamaki

@aureliagwen:

"Allah ya albarkace ki yar'uwa na sha fadama mutane cewa soyayya ta gaskiya eh akwai shi kuma na yarda da shi. Wannan baya la'akari da yanayi ko nauyin aljihu."

Ni ba ajinka bace: Budurwa ta ki amsa tayin auren saurayinta

A wani labari na daban, wata budurwa ta badawa saurayinta kasa a idanu bayan ya yi mata tayin son aurenta. Ta ce sam ita ba ajinsa bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel