Kotu Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Karar Neman Yin Babban Zaben 2023

Kotu Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Karar Neman Yin Babban Zaben 2023

  • Babban kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja ta yi watsi da wani karar da aka shigar na hana yin babban zaben 2023 kan kin barin yan Najeriya mazauna kasar waje yin zabe
  • Mai shari'a Inyang Ekwo, a sabon hukunci da ya yanke ya ce dokar kasar na yanzu bai bawa yan Najeriya mazauna kasashen waje damar kada kuri'a daga kasashen waje ba
  • Gabanin babban zaben shugaban kasar za a gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, alkalin a ranar Laraba, ya yi watsi da karar saboda rashin inganci

FCT, Abuja - A ranar Laraba, 15 ga watan Fabrairu, babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar na hana yin zabe kan dalilin hana yan Najeriya da ke kasashen waje yin zabe.

Kara karanta wannan

"Ka Bani Mamaki" Gwamna Wike Ya Maida Martani Ga Jawabin Shugaba Buhari Kan Karancin Naira

Da ya ke yanke hukuncin a ranar Laraba, Inyang Ekwo, mai shari'a, ya ce karar ba ta da inganci, kamar yadda wani rahoto da The Cable ta fitar ya tabbatar.

Mahmood
Kotu Ta Bada Hukuncin Karshe Kan Karar Neman Yin Babban Zaben 2023. Hoto: INEC
Asali: Facebook

Sabon hukuncin kotun na ranar Laraba

Alkalin yayin yanke hukuncin ya ce dokar Najeriya a yanzu ba ta bawa yan kasar mazauna kasashen ketare damar yin zabe ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta ce:

"Kotu ba ta yi dokoki. Ba za ta iya fadada doka ba domin wani batu da aka kawo gabanta komin tausayi ko wane hali abin ya ke."

Kuma, Tinubu ya sake ganawa da Buhari a yayin da kotu ta bawa CBN sabon umurni

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a fadar Villa a ranar Laraba 15 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya

A cewar The Punch, majiyoyi kwararra daga fadar shugaban kasa sujn ce an yi taron ne a ofishin Buhari, hakan yasa Buhari ya makara zuwa taron majalisar tattalin arziki na kasa da kimanin mintuna 40.

An rahoto cewa Buhari ya iso dakin taron misalin karfe 10.40 na safe, kimanin awa guda bayan lokaci da ya dace a fara taron.

Gwamna Sanwo-Olu ya dage yakin neman zabensa har sai baba ta gani

A baya kun ji cewa gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya dage yakin neman zabensa gabanin babban zaben da ke tafe.

Gwamnan ya sanar da cewa ya dauki wannan matakin ne domin tausayawa yan jiharsa bisa karancin man fetur da takardun naira da ake fama da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel