Katsalandan: Gwamna Wike Ya Yi Martani Ga Jawabin Buhari Kan Naira

Katsalandan: Gwamna Wike Ya Yi Martani Ga Jawabin Buhari Kan Naira

  • Gwamna Wike na jihar Ribas ya yi martani kan jawabin da shugaban kasa ya yi kai tsaye ga yan Najeriƴa
  • Wike, mamban jam'iyyar PDP, ya ce ko kaɗan bai taba tsammanin Buhari zai yi katsalandan ga bangaren shari'a ba
  • Ya kuma shawarci na kusa da shugaban kasa su ankarar da shi kuskuren da ya yi domin ya gyara

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya soki matakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na haramta amfanin tsoffin takardun N500 da N1000 a jawabinsa na ranar Alhamis.

Wike ya ce kuskure ne shugaba Buhari ya yi haka duk da umarnin Kotun koli wanda ya bayyana cewa dukkan takardun naira su ci gaba da amfani har zuwa lokacin da zata yanke hukuncin ƙarshe.

Gwamna Wike.
Katsalandan: Gwamna Wike Ya Yi Martani Ga Jawabin Buhari Kan Naira Hoto: thenation
Asali: UGC

Channels tv tace gwamnan Ribas ya faɗi haka ne yayin hira da kafafen watsa labarai jim kaɗan bayan jawabin da shugaban kasa ya yi kai tsaye ga yan Najeriya ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Ya Sabawa Kotun koli Wajen Dawo da Tsofaffin N200 Daga Hannun CBN

Ya ayyana matsayar Buhari ta halatta amfani da N200 da kuma haramta N500 da N1000 da, "Katsalandan" inda ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tun da Kotun koli ta ba da umarnin cikin shari'a ya kamata mu jinkirta zuwa lokacin. A iya abinda na sani wannan shiga sharo ba shanu ne wanda ba abu ne mai kyau ba ga tsarinmu, Dimukraɗiyyar mu."

Wike ya ƙara da cewa duk da an ɓullo da tsarin sauya naira ne da nufin wasu mutane amma lokaci da kuma hanyar aiwatar da shi kuskure ne.

Gwamnan Ribas ya ce ya yi tsammanin shugaban ƙasa Buhari zai yi biyayya ga Umarnin Kotun Allah ya isa, ba zai tsoma baki ba.

"Kotu lamba ɗaya a kasar nan ta yi magana, Kotun koli tace karku yi wani abu da zai shafi amfanin tsoffin takardun kuɗi. Ina ganin (Kalaman shugaban kasa) bai dace ba kuma ban ji daɗi ba."

Kara karanta wannan

Tattaunawa: Lauya Ya Shawarci INEC Kan Yadda Zasu Dakile Sayen Kuri'u

Gwamnan na jam'iyyar PDP ya ce ya kamata mashawartan shugaban kasa su gaggauta ankarar da shi, ya girmama umarnin Kotun koli, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Mutane sun fara lalata bankuna

A wani labarin kuma Fusatattun Mutane Sun Babbake Bankuna a Jihar Delta Saboda Karancin Naira

Rahotanni sun bayyana cewa yan Najeriya sun fusata da halin ƙuncin da karancin takardun naira ya jefa su, sun barke da zanga-zanga.

Gwamna Okowa ya yi kira ga mazauna Delta da Najeriya baki ɗaya su kara hakuri domin masu alhaki kan lamarin suna iya bakin kokarinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel