Kakakin Majalisar Tarayyar Najeriya Ya Bayyana Wadanda Suka Janyo Karancin Naira Da Fetur

Kakakin Majalisar Tarayyar Najeriya Ya Bayyana Wadanda Suka Janyo Karancin Naira Da Fetur

  • Shugaban majalisar wakilai ya bayyana cewa wasu bata gari ne suka janyo wahalar man fetur da karancin kudi
  • Gbajabiamila ya bayyana haka a wajen taron rabon tallafin motocin sufuri ga al'ummar mazabarsa
  • Ya kuma kara da cewa anyi hakan ne da nufin dakile Asiwaju Bola Tinubu zama shugaban kasa a zaben shugaban kasa na 25 ga watan Fabrairu

Legas - Kakakin majalisar wakilai, Mr Femi Gbajabiamila, ya alakanta karancin man fetur da kuma kudi a da ayyukan 'yan neman hana ruwa gudu', rahoton The Punch.

Ya bayyana haka a Lagos ranar Talata, lokacin da yake kaddamar da kashi biyu na rabon kayan sufuri na ''Gbaja ride.''

Shirin wanda aka kaddamar da nufin tallafawa yan mazabarsa ta Surulere.

Gbajabiamila
Kakakin Majalisar Tarayyar Najeriya Ya Bayyana Wadanda Suka Janyo Karancin Naira Da Fetur. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito an raba motoci masu saukin farashi guda 35 da za su zaga sassa daban daban na Surulere da kewaye.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisa Ya Fallasa Masu Hannu Dumu-Dumu a Canjin Kudi da Wahalar Fetur

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan neman hana ruwa gudu ne suka janyo karancin man fetur da sabbin naira, Gbajabiamila

Gbajabiamila ya bayyana karancin man fetur da rashin kudi a hannun mutane wasu 'yan hana ruwa gudu' ne suka kirkira da nufin kawo koma baya ga nasarar shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Da yake jawabi a wajen ''Gbaja ride'' ya bayyana cewa an fara shirin tun watan Yunin 2018 da sabbabin motoci 30, babura 160 da kuma babura masu kafa uku 25.

Ya ce a karo na biyu na kaddamar da shirin an yi kyakkyawan tsari don raba motocin sufuri masu arha don tallafawa al'ummar Surulere.

Gbajabiamila ya ce sabbin motocin 35 za suyi aiki tare da kungiyoyin tasha da kuma gareji.

Ya kuma bayyana cewa, motocin za su dinga daukar malamai kyauta, hadi da dalibai da kuma tsofaffi da suka haura shekara 70.

Kara karanta wannan

Bayan Zaman Kotun Koli, CBN Ya Sake Magana Kan Masu Sayar da Sabbin Naira

Ya ce shirin daya ne daga daga cikin ayyukan sa da dama da nufin inganta rayuwar al'ummar mazabarsa.

Majalisa za ta yi aiki don ceto Najeriya, Gbajabiamila

Ya ce majalisar wakilai tana aiki tukuru don ceto yan Najeriya daga halin matsin matsin da suke ciki tare da kawo sauki nan ba jimawa ba.

''A matsayina na wakilinku kuma shugaban majalisa, ina da kyakkyawar fahimtar halin matsi da rashin jin dadi da aka jefa yan Najeriya ciki, hadda yan mazaba ta.
''Majalisar wakilai karkashin jagoranci na tana bayan al'umma, tare da aiki tukuru don ceto su daga halin kuncin da ake ciki.
''Ina farin ciki cewa bangaren shari'a ya goyi bayan matakin da muka dauka kan dokar chanjn kudu.''

Shugaban majalisar ya kuma zargi wasu bara gurbi sun kirkiri dokar don dakile dan takarar shugabancin kasa na APC, Bola Tinubu, daga cin zaben shugaban kasa mai zuwa.

Kara karanta wannan

Toh fa: Atiku da Tinubu sun tsufa, dattawan Arewa sun fadi mafita a zaben 2023

Ya ce:

''Ba wanda zai iya gamsar dani cewa ba yi aka yi don hana Asiwaju zama shugaban kasa a kasar nan ba.
''Amma naji dadi kasancewar Allah ya kawo dauki, saboda ya tona asirin su.
''Na bi taron gangamin yakin neman zabe zuwa Gabas, Arewa da kuma ko ina tare da Asiwaju kuma na jinjinawa yan Najeriya.''

Tun a farko, shugaban karamar hukumar Surulere, Sulaiman Yusuf, ya yabawa kokarin Gbajabiamila kan tallafin.

Ya ce shirin karin hujja ce ta cewa kakakin majalisar ya damu da rayuwar al'ummar mazabarsa.

A cewarsa:

''Wannan wata hujja na cewa kakakin majalisar ya damu da mu. Yayi wa al'ummar Surulere aiki kuma muna alfahari da shi."

Gidan mai da yan kasuwa suna kin karbar tsohon kudi a Sokoto

A wani rahoton kun ji cewa wasu bankuna da bankuna da kantuna suna kin karbar tsaffin takardun naira a jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel