CBN Ya Bayyana Yadda Mutane Zasu Kai Rahoton Masu POS Din Dake Sayar da Sabbin Naira

CBN Ya Bayyana Yadda Mutane Zasu Kai Rahoton Masu POS Din Dake Sayar da Sabbin Naira

  • Babban Bankin CBN ya saki lambobin da mutane za su kira don yin karar masu siyar da kudi
  • CBN ya kuma bukaci jama’a da su kira lambobin wayarsu don fallasa masu POS da ke chajin kudi da yawa
  • Yan Najeriya na ci gaba da fama da rashin sabbin naira yayin da sabis din transfa ke kara tabarbarewa

Bayelsa - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya saki lambobin wayar gaggawa ga jama'a don kai rahoton masu POS da ke siyar da sabbin naira da kuma wadanda ke chajin kudi da yawa yayin cire kudi.

Daraktan Sashen Gwamnan CBN, Mista Josph Omayuku, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa a ranar Talata, 14 ga watan Fabrairu, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun koli ya dage karar gwamnoni 12 da CBN kan batun wa'adin tsoffin kudi

Kudi da POS
CBN Ya Bayyana Yadda Mutane Zasu Kai Rahoton Masu POS Din Dake Sayar da Sabbin Naira Hoto: Punch
Asali: UGC

Yayin da yake gargadin masu aikata abubuwan da basa bisa ka'ida a kan su daina, Omayuku ya shawarci jama'a da su kai karar masu POS da ke tatsar su ta hanyar kiran CBN a lambobi kamar haka 07002255226; Ext: 711025 – 7; contactcbn@cbn.gov.ng da shafukansu na soshiyal midiya.

Karancin takardun naira na kara jefa yan Najeriya cikin wani hali inda mutane da dama ke kin amsar tsoffin kudi, yayin da wasu gwamnoni suka yanke shawarar maka gwamnatin tarayya a kotu don kalubalantar halin da ake ciki a jihohinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rashin kyan sabis na hana yan Najeriya karbar transfa

Duk da mawuyacin halin da manufar sauya kudin ya jefa mutane a ciki, har yanzu akwai korafe-korafe kan rashin karfin sabis a tsarin biyan kudade ta yanar gizo wanda hakan ya sa ba a iya yin hada-hadar kudi ta hanyar transfa.

Kara karanta wannan

Matsayar Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi a kan batun Canjin N200, N500 da N1000

Masu lura sun ce hakan na faruwa ne saboda dandamalin sadarwa ta kasar basu da karfin da za su iya daukar hada-hadar kudi ta yanar gizo a baya-bayan nan yayin da mutane suka koma yin kasuwanci ta hanyar transfa don saukaka rashin tsabar kudi.

Wadanda ke kin karbar transfa sun bayyana matsalolin da ke tattare da tsariin a matsayin dalilinsu na kin yarda da shi.

Sai dai kuma, jami'in CBN din ya yi tir da haka, yana mai cewa lamarin bai yi muni da har zai sa a ki karbar transfan kudi ba, rahoton Punch.

Matashi ya yi wanka da soso da sabulu a gaban banki, yana jiran a bashi kudinsa

A wani labari, wani matashi ya yi abun ban mamaki yayin da ya isa banki da bokitin ruwa da kwaryar soso da sabulunsa sannan ya dirje jikinsa a gaban wani banki.

Baya ga haka, ya tanadi tabarma da yar jaka da ya zuba abubuwan bukatarsa yayin da yake zaman jiran jire kudinsa daga banki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel