Atiku da Tinubu Sun Tsufa, Dole Su Samu Nagartattun Mutane a Gefensu, Inji Dattawan Arewa

Atiku da Tinubu Sun Tsufa, Dole Su Samu Nagartattun Mutane a Gefensu, Inji Dattawan Arewa

  • Zauren Dattawan Arewa (NEF) ya bayyana cewa, 'yan takarar shugaban kasa a APC da PDP sun tsufawa mulkin Najeriya
  • Dr Hakeem Baba Ahmad ne ya bayyana hakan a cikin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin
  • Ya fadi abin da 'yan takarar biyu ke bukata idan suka samu nasarar gaje kujerar Buhari a zaben 2023 na bana

Daraktan yada labarai na Zauren Dattawan Arewa (NRF), Dr. Hakeem Baba Ahmad ya ce, ‘yan takarar shugaban kasa na APC; Bola Ahmad Tinubu da PDP; Atiku Abubakar sun tsufa.

Baba Ahmad ya bayyana hakan ne yayin wata tattauna kan zaben 2023 da ya yi da gidan talabijin na Channels a ranar Talata.

Ya bayyana cewa, Atiku da Tinubu suna bukatar mutanen da ke da gogewa a fannin nagartar tafiyar da mulki idan aka zabi dayansu a zaben 2023 da ke tafe.

Kara karanta wannan

Shin karancin Naira zai shafi zaben bana? Jami'in INEC ya yi gargadi mai daukar hankali

Arewa ta bayyana cewa Tinubu da Atiku sun buya
Atiku da Tinubu Sun Tsufa, Dole Su Samu Nagartattun Mutane a Gefensu, Inji Dattawan Arewa | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Halin da Tinubu da Atiku ke ciki

A kalamansa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Da yawan wadanda ke kan gaba a yanzu sune Atiku da Tinubu kuma sun tsufa kuma duk kokarinsu, ba za su iya yin komai da suke so ba.
“Suna bukatar wasu nagartattun mutane a kusa dasu, mutanen da ke ilimin yadda za a gyara Najeriya. Wannan ne abu mai muhimmanci.
“Abu na biyu shine samu mutane masu nagarta, ba wadanda za su mayar da kudin gwamnati aljihunsu ba.
“Ya kamata su kasance nagari, kwararru masu tunani kuma mutanen da ke shaidar tsoron Allah.

Kungiyoyi dai na ci gaba da bayyana sharhinsu kan 'yan takarar da suka nuna sha'awar gaje kujerar Buhari a zaben 2023 da ke tafe nan ba da jimawa ba.

Buhari abin koyi ne ga dukkan wanda ya gaji kujerarsa a zaben 2023 da ke tafe, inji Boss Mustapha

Kara karanta wannan

Sai Kin Biyani N10m Zan Sake Ki: Wani Ango a Kano Ya Bukaci Sabuwar Amarya Mai Neman Saki

A wani labarin kuma, kunji yadda sakataren gidan gwamnatin Najeriya ya bayyana irin kokarin da gwamnatin Buhari ta yi na tsawon lokaci tun hawanta zuwa yanzu.

Boss ya bayyana cewa, mulkin Buhari babban abin koyi ne ga dukkan wanda Allah ya ba nasara ya lashe zaben 2023 da ke tafe nan ba da jimawa ba.

A cewarsa. gwamnatin ta jure abubuwa da yawa, kuma ya kamata a ci gaba daga inda ta tsaya ta hanyoyi daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel