Shugaban Majalisa Ya Fallasa Masu Hannu Dumu-Dumu a Canjin Kudi da Wahalar Fetur

Shugaban Majalisa Ya Fallasa Masu Hannu Dumu-Dumu a Canjin Kudi da Wahalar Fetur

  • Shugaban majalisar wakilan tarayya ya ce sauya kudi tsari ne mai kyau da wasu suka lalata shi
  • Rt. Hon. Femi Gbajabiamila yana ganin masu wannan su na yi wa Bola Tinubu zagon-kasa ne
  • ‘Dan siyasar ya ce duk da kutun-kutun da ake yi, ‘dan takaran APC yana ya samun karbuwa a kasa

Lagos - Shugaban majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila ya na ganin akwai wadanda ke da hannu wajen matsin lambar tattalin arziki.

Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya zargi wasu masu hana ruwa gudu da laifi wajen kawo wahalar man fetur da kuma karancin takardun kudi a kasa.

Da yake magana wajen kaddamar da ayyuka a mazabarsa, Vanguard ta rahoto Gbajabiamila a ranar Talata yana zargin wasu da zagon-kasa.

Gbajabiamila ya fito da tsarin ‘Gbaja Ride’ domin saukake zirga-zirga a mazabarsa ta Surulere.

Kara karanta wannan

Matsayar Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi a kan batun Canjin N200, N500 da N1000

‘Dan majalisar tarayyar ya ce wasu miyagu ne suka yi kutun-kutun jawo wahalar man fetur a gidajen mai da kuma karancin takardun Nairori.

Na san ana wahala - Gbajabiamila

"A matsayin wakilinku kuma Shugaban majalisa, na fahimci halin da da-dama daga cikin ‘Yan Najeriya suke ciki, har da ‘yan mazabata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bola Tinubu
Bola Tinubu a Katsina Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Majalisar wakilan tarayya a karkashin jagorancina ta na tare da jama’a, mu na aiki dare da rana domin ceto su daga wahalhalun da ake ciki.
Ina farin ciki da kotu ta tabbatar da matsayarmu a game da batun dabbaka tsarin canza Nairori.

- Femi Gbajabiamila

Daily Post ta rahoto Shugaban majalisar yana mai cewa sauya kudi tsari ne mai kyau da wasu suka yi amfani da shi, suka kawo siyasa a cikin lamarin.

Zargin da ‘dan siyasar yake yi shi ne an jagwalgwala tsarin saboda a hana Bola Tinubu yin nasara, ya ce duk da haka ana karbar ‘dan takaran na APC.

Kara karanta wannan

Toh fa: Atiku da Tinubu sun tsufa, dattawan Arewa sun fadi mafita a zaben 2023

Babu wanda zai fada mani ba manufa ce aka kitsa domin hana Asiwaju zama shugaban kasar nan ba. Amma Ubangiji ba ya barci, ya kawo mafita.
Na je yawon kamfe a Gabas, Arewa da ko ina tare Asiwaju, kuma ‘Yan Najeriya na karbar shi."

- Femi Gbajabiamila

Lissafin PDP a 2023

An samu labari cewa Dele Momodu wanda Darektan kamfe ne a PDP yana hasashen Atiku Abubakar zai yi galaba a jihohin Arewa da Kudancin Najeriya.

Momodu ya ce Atiku zai samu 25% a duk jihohin Arewa kuma ya samu kaso mai tsoka a jihohi 24 da ake nema, hakan zai ba shi damar doke APC da LP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng