Sokoto: Gidajen Mai, Yan Kasuwa Da Bankuna Sun Dena Karbar Tsaffin Takardun Naira

Sokoto: Gidajen Mai, Yan Kasuwa Da Bankuna Sun Dena Karbar Tsaffin Takardun Naira

  • Rahotanni daga Jihar Sokoto sun bayyana cewa bankuna da sauran wuraren kasuwanci sun daina karbar tsohon kudi
  • Wani ma'aikacin banki ya shaida cewa matakin na zuwa ne biyo bayan umarnin da babban bankin kasa CBN ya turo da shi
  • Al'umma na cigaba da kokawa kan yadda gwamnatin tarayya ta ki jin koken talakawa akan batun chanjin kudi

Sokoto - Wasu masu gidanjen mai, yan kasuwa da kuma bankunan kasuwanci sun kauracewa umarnin kotun koli da kuma shawarwarin hukumomin kasa akan dokar sabon kudi, inda suke cigaba da kin karbar tsohon kudi a Jihar Sokoto.

Rahotanni daga The Punch sun tabbatar cewa da yawa daga cikin bankunan kasuwanci a jihar ba sa karbar tsohon kudi daga abokan huldar su.

Tsaffin Naira
Gidajen Mai, Yan Kasuwa Da Bankuna Sun Dena Karbar Tsaffin Takardun Naira A Sokoto. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Yan Kasuwa Da Direbobi Na Cigaba Da Kin Karbar Tsohon Kudi Duk Da Umarnin Kotun Koli

Wani abokin huldan banki, wanda ya shaidawa majiyar, ya ce:

''Ina banki da safiyar nan don ajiye kudi amma babban abin mamaki, masu karbar kudin sun ki karbar tsofaffin kudin mu.
''Mun yi kokarin yin magana da shugaban reshen, wanda ya shaida mana cewa babban bankin kasa CBN ya turo da umarnin a daina karbar tsohon kudi.
''Abin takaici ne hukumomin da ke karkashin gwamnatin tarayya suki bin umarnin da kotu ta ba su, hakan ba daidai bane.''

Sannan, an ruwaito cewa da yawa daga cikin gidajen mai, musamman babban kamfanin mai na kasa NNPC sun ki karbar tsofaffin kudin a hannun abokan hulda.

Wannan dalilin kamar yadda rahotanni suka bayyana ka iya janyo karuwar yanayin rudanin da ake ciki a jihar.

Wani mazaunin garin Sokoto ya magantu kan dena karbar tsohon kudin

Wani mazaunin jihar da ya zanta da wakilin majiyar Legit ya yi Allah wadai da matakin babban bankin kasa CBN da kuma gwamnatin tarayya na rashin sauraren koken talakawa a kasar.

Kara karanta wannan

Ci gaba da kashe tsoffin Naira: Bankuna sun yi magana bayan hukuncin kotun koli

A cewarsa:

''Abin da yake shirin faruwa zai iya zama mai muni fiye da zanga-zangar 'End SARS, wanda ya jawowa kasar koma baya.
''Ina shawartar gwamnati da ta dauki matakin da ya dace kafin yan Najeriya su kai bango su fara daukar mataki.''

Haka, da yawan yan kasuwa, musamman wanda ke tsofaffin kasuwannin jihar, sun bi sahu wajen kin karbar kudin daga hannun abokan huldar su.

Wani rahoto daga jihar ya kuma bayyana cewa daya daga cikin masu manyan katafaren kasuwannin zamani da aka fi sani da Alhaji Yaro Gobirawa ya dena karbar tsohon kudi a jihar.

Gobirawa, wanda shine tsohon shugaban kungiyar yan kasuwa a jihar, yana daya daga cikin wakilan da suka zauna da babban bankin kasa CBN a jihar da shawo kan matsalar karancin takurdun Naira.

Daya daga cikin ma'aikatan kasuwar zamanin a zantarwar sa da The Punch ya tabbatar da an dauki matakin biyo bayan daina karbar tsohon kudi da bankuna suka yi daga hannun abokan huldar su.

Kara karanta wannan

Naira: El-Rufa'i Da Yahya Bello Sun Dira Kotun Koli Inda Za'a Yanke Hukunci Yanzu

A bangare guda, kun ji cewa bankuna a wasu jihohin sun bijirewa umurnin babban bankin Najeriya, CBN, sun cigaba da karbar tsohon kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel