2023: Gwamnan Ebonyi Ya Bayyana Katafaren Aikin Buhari Ya Yi Da Yasa Ibo Za Su Zabi Tinubu Da Jam'iyyar APC

2023: Gwamnan Ebonyi Ya Bayyana Katafaren Aikin Buhari Ya Yi Da Yasa Ibo Za Su Zabi Tinubu Da Jam'iyyar APC

  • Gwamnonin kabilar Igbo sun tabbatar wa Tinubu cewa shine zai lashe yankin
  • Sun bayyana haka ne lokacin da yake taron yakin neman zabe a Owerri babban birnin Imo
  • A nasa bangaren Tinubu ya ce zai tabbatar da cigaban Imo da sauran sassan kasar nan

Owerri, Imo - Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya ce kabilar Ibo za su zabi APC da dan takarar ta, Bola Tinubu, saboda gina gadar Niger ta biyu da akayi a zamanin Shugaba Muhammadu Buhari.

Umahi ya bayyana haka a taron gangamin APC na kudu maso Gabas a Owerri ranar Talata, rahoton The Punch.

Dave Umahi
2023: Gwamnan Ebonyi Ya Bayyana Babban Dalilin Da Yasa Ibo Za Su Zabi Tinubu Da Jam'iyyar APC. Hoto: Peoples Gazette
Asali: Facebook

Gina gadar Neja ta biyu da Buhari ya yi zai sa Ibo su sake zaben APC, Umahi

Umahi, da yake shaida cewa kudu maso Gabas suna yaba wa shugaban kasa saboda aikin yana cewa, ''Ibo za su zabi APC saboda aikin gadar da Muhammadu Buhari ya yi.''

Kara karanta wannan

Buhari Bai Yi Kokari Sosai a Nan ba, Jigon APC Ya Fadi Bangare 1 da Tinubu Zai Gyara

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shi ma gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya tabbatarwa da jam'iyyar cewa APC za ta cinye jihar a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Fabrairu.

Uzodimma ya ce:

''Mutanen Imo suna godiya ga shugaban kasa. Mun nemi gudunmawar ka don gina hanyoyi da kuma yakar rashin zaman lafiya a Imo kuma ka bamu. Lokacin dawo da alkhairin ya yi ta hanyar zabar APC.''

Sannan, Gwamna Babajide Sanwu-Olu na Jihar Lagos, ya ce gaba daya yan kabilar Ibo mazauna kudu maso yamma suna son Tinubu kuma shi zasu zaba.

Tinubu, da yake magana a taron, ya bayyana cewa, idan aka zabe shi, gwamnatin sa za ta cigaba ayyukan ci gaba na shugaban kasar. Ya kuma ce zai kara kimar gidaje da kuma tallafawa ilimi a jihar.

Za mu cigaba da ayyukan alheri da APC suka fara - Tinubu

Kara karanta wannan

Sarkin Ibo Ya Yi wa Shugaban Kasa Abin da ba Zai Manta ba Har ya Bar Duniya

Tinubu ya ce:

''PDP sun sace arzikin kasa. Shekara takwas din Buhari kokarin dawo da arzikin kasa yake. PDP makaryata ne. Za mu cigaba da ayyukan ci gaba na APC, ba za mu tsaya ba.
''Imo cibiyar yawon bude ido ce, zamu kara kawata gine-ginen Jihar Imo, mu tallafawa ilimi, mu gina sababbi da kuma gyara titunan Imo. Ba maganar yajin aikin ASUU. Zamu habbaka mu kuma daidata tara kudin shiga, zamu kawo zaman lafiya, zamu muyi da gwamnatin jiha don tabbatar da zaman lafiya.''

Ministan Labarai Lai Mohammed ya fadi babban nasarar da ya samu

An kuma ji cewa Lai Mohammed, ministan labarai da al'adu ya ce kwato kayan tarihi da al'ada na nahiyar Afirka daga kasashen waje shine babban nasarar da ya samu a matsayinsa na minista.

Asali: Legit.ng

Online view pixel