Shugaban Kasa a 2023: Lokaci Ya Yi Da Za a Saka Wa Tinubu, Gamayyar Kungiyoyin Arewa

Shugaban Kasa a 2023: Lokaci Ya Yi Da Za a Saka Wa Tinubu, Gamayyar Kungiyoyin Arewa

  • Gamayyar kungiyoyin yan arewa sun yi muhimman zantuka yan kwanaki kafin zaben shugaban kasa na 2023
  • Kungiyar arewar ta ce yanzu lokaci ne da yan arewa za su saka wa Bola Tinubu na APC da alkhairin da ya yi masu
  • Saura kwanaki 11 a zabi magajin Shugaba Buhari tsakanin Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso

Katsina - Gamayyar kungiyoyin arewa a jihar Katsina, sun bayyana zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin lokacin saka wa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kungiyar ta bayyana cewa Tinubu ya taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran shugabannin arewa, jaridar The Nation ta rahoto.

Bola Tinubu
Shugaban Kasa a 2023: Lokaci Ya Yi Da Za a Saka Wa Tinubu, Gamayyar Kungiyoyin Arewa Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Tun 1999 Tinubu ke tare da al'ummar arewa

Yayin wani taron tattaunawar kwana daya na kungiyar Tinubu/Shetima tare da kungiyoyin addinai da aka yi a Katsina a jiya Litinin, jagoran kungiyar, Kwamrad Hamza Umar Salauwa, ya jaddada cewar tun 1999 Tinubu ke tare da Arewa.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Wakilta Pantami, Ya Faɗi Wanda Shugaban Kasa Ke Goyon Baya 100 Bisa 100 a Zaben 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Idan ya zama dole mu tabbatar da adalci da gaskiya, toh dole mu marawa takarar shugabancin Tinubu baya kamar yadda muka yi wa marigayi MKO Abiola da Babagana Kingibe.
"Har gobe Tinubu ne zabin Arewa, da Hausa Fulani. Idan muka gaza, ba za mu taba sake amfana daga Lagas ba.
"Yanzu ne lokacin da yakamata arewa ta saka wa dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta hanyar basa kuri'u masu yawan gaske a matsayin shugaban kasar Najeriya na gaba.
"Mun tuna yadda Tinubu ya marawa dan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar baya lokacin da ya nemi takarar kujerar a karkashin rusasshiyar jam'iyyar ACN da kuma yadda ya marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya wajen lashe zabe a karkashin jam'iyyar APC. Yanzu lokacin Tinubu ne na zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Ba Gwamnan Arewan da Zai Iya Kawowa Tinubu Kuri'un Jiharsa, Tsohon Shugaban NHIS

"Tinubu na son arewa kuma idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, zai bunkasa ra'ayin arewa."

Ya kuma ba yan Najeriya tabbacin cewa idan aka zabe shi, Tinubu zai maimata irin kyawawan ayyukan da ya yi a Lagas a fadin Najeriya.

A gefe guda, jaridar Vanguard ta rahoto cewa harkoki sun tsaya cak yayin da dandazon magoya baya suka fito da yawansu don nuna goyon bayansu ga Asiwaju Bola Tionubu a zaben shugaban kasa na 2023, a yankin Ikorodu ta jihar Lagas.

Duk da Buhari na goyon bayansa, Katsinawa ba za su zabi Tinubu ba - Tsohon shugaban NHIS

A wani labarin, tsohon shugaban hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf, ya bayyana cewa Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC ba zai kawo jihar Katsina ba.

Farfesa Yusuf ya ce duk da cewar Shugaba Muhammadu Buhari na goyon bayansa, Katsinawa ba za su zabe shi ba a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel