Ina Goyon Bayan Tinubu 100% Ya Zama Shugaban Kasa a 2023, Buhari

Ina Goyon Bayan Tinubu 100% Ya Zama Shugaban Kasa a 2023, Buhari

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya karyata masu yaɗa ƙanzon kurege cewa ba ya kaunar Bola Tinubu ya gaje shi a 2023
  • A wurin ralin kamfe a Gombe, Buhari ya kara jaddada cikakken goyon bayansa ga Tinubu 100% da dukkan yan takarar APC
  • Buhari ya kuma roki yan Najeriya da su zabi Tinubu ya zama shugaban kasa domin kawo ci gaba

Gombe - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ƙara jaddada cikakken goyon bayansa 100% ga Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Buhari, Sanata Ahmad Lawan da wasu gwamnonin APC sun mamaye Gombe domin halartar rali da kuma kaddamar da kwamitin kamfen Tinubu/Shettima a jihar.

Tinubu da tawagarsa a Gombe.
Ina Goyon Bayan Tinubu 100% Ya Zama Shugaban Kasa a 2023, Buhari Hoto: Bola Tinubu
Asali: Facebook

A filin wasan Pantami wurin gudanar da Ralin APC ranar Litinin, Shugaba Buhari ya bukaci mazauna jihar Gombe su zabi Bola Tinubu da sauran yan takarar jam'iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Suna Ya Fito: Atiku Ya Yi Alkawarin Sako Shugaban Kungiyar Ta'addanci a Najeriya Idan Ya Ci Zaben 2023

Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Farfesa Isa Pantami, ya ce raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ba ya goyon bayan Tinubu ba gaskiya bane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙasan ya bayyana cewa zai ci gaba da aiki ba kama hannun yaro wajen tabbatar da nasarar Tinubu da kuma APC a babban zaɓen 25 ga watan Fabrairu.

Gwamnan Filato kuma DG na kamfen Tinubu/Shettima, Simon Lalong, ne ya sanar da cewa Buhari ya wakilto Pantami a wurin taron, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

A jawabinsa, Shugaba Buhari ya ce:

"Ina goyon bayan baki ɗaya 'yan takarar da jam'iyyata ta tsayar kuma ina tare da ɗan takarar mu na shugaban ƙasa 100% babu sirki. Saboda haka duk wanda ya zo ya faɗa muku saɓanin haka ƙarya yake."

Bugu da ƙari, Buhari ya ambaci wasu ayyukan alheri da gwamnatin tarayya ta zuba wa mutanen Gombe, ciki har da haƙo ɗanyen mai, wanda ya ce an gano shekaru 40 da suka gabata.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Tinubu Ya Jawo Hadimansa Suna Cin Mutuncin Shugaban kasa - Atiku

Ba'a Taba Gwamnan CBN Mai Kawo Rudani Irin Emefiele Ba - Adeyeye

A wani labarin kuma Tsohon karamin minista a Najeriya yace gwamna CBN ya kafa tarihin zama mafi haddasa ruɗani

Dayo Adeyeye, shugaban ƙungiyar magoya bayan Tinubu a kudu maso yamma SWAGA, ya ce duk da boyayyar manufar Emefiele, Tinubu zai samu nasara a 2023.

A cewarsa, a tarihin Najeriya ba'a taba samun gwamnan CBN mai haddasa rudani da kuntatawa jama'a ba kamar Emefiele.

Asali: Legit.ng

Online view pixel