El-Rufai Ya Kara Tonon Silili, Ya Fallasa Burin Wadanda ke Zagaye da Buhari a Zaben 2023

El-Rufai Ya Kara Tonon Silili, Ya Fallasa Burin Wadanda ke Zagaye da Buhari a Zaben 2023

  • Gwamnan jihar Kaduna ya sake caccakar mutanen da ke zagayen shugaba Muhammadu Buhari
  • Malam Nasir El-Rufai yake cewa burin wadannan miyagu shi ne kafa gwamnatin rikon kwarya
  • A tattaunawar karshe da aka yi da shi, El-Rufai ya kara nuna bai jin tsoron fallasa masu aikin nan

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi wata kebantaciyyar hira, a nan ya ce akwai masu neman kafa gwamnatin rikon kwarya a Mayu.

Malam Nasir El-Rufai ya zargi wasu da ba su rike da mukaman gwamnati da kokarin kawo matsala a zaben sabon shugaban kasa mai zuwa da za a shirya.

Gwamnan ya ce wadanan mutane sun kirkiro hanyoyin kifar da gwamnati ko su hana a mika mulki salin-alin ga wanda zai zama sabon shugaban kasa.

Fitaccen gwamnan bai iya kama sunan wadannan mutane a tattaunawarsa da Premium Times ba, sai dai ya ce ba su kai a kira su da wasu miyagu ba.

Kara karanta wannan

Da Gaske Matasa Sun Yi Wa Gwamna Buni Ruwan Duwatsu? Gwamnatin Yobe Ta Bayyana Gaskiyar Lamari

El-Rufai bai yi masu kallon kowa

A cewarsa, miyagun da ke rike madafan iko su na zuwa da wani salo da tsari na dabam, abin da mutanen da ke zagaye da Muhammadu Buhari suka rasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk da haka, Gwamnan ya nuna bain jin tsoron tona masu asiri, ya fadi sunansu gaban Duniya.

Shugaban Kasa
Muhammadu Buhari wajen zabe Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images
“Ba ni da matsalar kama sunan su. Ba na tsoron kowa. Amma a wurina, fadan sunansu tamkar taimaka masu ne, Ba kowan kowa ba ne.
Ba za su iya cin zabe ba. Ba su da nauyi a siyasa ko a filin zabe. Sai dai su fake a bayan irinsu Buhari domin cin ma manufa da burinsu."

- Malam Nasir El-Rufai

Buhari yana tare da APC?

Tsohon Ministan birnin tarayyan kasar yake cewa duk abin da zai faru, ya tabbata shugaba Buhari ba zai taba yakar Bola Tinubu, ya hana shi mulki ba.

Kara karanta wannan

Na Daina Aminta da Nagartar Mutanen Dake Kewaye da Buhari, El-Rufai Ya Kara Fasa Kwai a Aso Villa

"A wajen Buhari, an haifi APC ne bayan an yi cikin shekara da rabi. Zan rantse, ba zai taba yi wa APC zagon-kasa ba, ko da shaidan ne ‘dan takaran APC.
Abin da yake faruwa, su na da ‘yan takara biyu da suke so su gaji Buhari - Godwin Emefiele a Kudu da Ahmad Lawan a Arewa, babu wanda ya yi nasara."

- Malam Nasir El-Rufai

Sarautar Jagaban da aka ba Tinubu

A wani rahoto da aka fitar, kun ji yadda Mai martaba, Alhaji Haliru Dantoro Kitoro III [Mai Borgu] ya ba Bola Tinubu sarautar Jagaban na kasar Borgu.

Uwargidar Gwamnan Legas ta lokacin, Sanata Remi Tinubu ta zama Yun Bana a kasar Borgu. Bayan shekaru 9 da nadin sarautar, Sarkin ya rasu

Asali: Legit.ng

Online view pixel