Babu Wanda Ya Jefe Ni Da Duwatsu a Wajen Gangamin Siyasa – Gwamna Buni

Babu Wanda Ya Jefe Ni Da Duwatsu a Wajen Gangamin Siyasa – Gwamna Buni

  • Gwamnatin Yobe ta ce babu wani hari da aka kai a wajen gangamin kamfen din APC da ya gudana a Gashua, karamar hukumar Bade ta jihar
  • Kakakin Gwamna Mai Mala Buni ya ce babu wanda ya yi wa ubangidansa ruwa duwatsu a yayin kamfen din
  • Mamman Mohammed ya ce wasu kungiyoyi biyu ne suka kara a tsakaninsu bayan ma gwamnan ya bar Gashua

Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, Ya Yi watsi da rade-radin da ke yawo cewa wasu fusatattun matasa sun yi masa ruwan duwatsu a wajen wani gangamin siyasa da ya gudana a jihar, Arise News ta rahoto.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da sauran mambobin kwamitin yakin neman zaben APC sun halarci gangamin kamfen din.

Gangamin APC a Yobe
Babu Wanda Ya Jefe Ni Da Duwatsu a Wajen Gangamin Siyasa – Gwamna Buni Hoto: The Cable
Asali: UGC

Sai dai an yi ikirarin cewa wasu sun kai wa gwamnan na jihar Yobe hari a yayin taron, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kungiyar CAN Ta Yi Wa Masari Wani Karamci Da Bata Taɓa Yi Wa Kowa Ba A Tarihi Tun Kafuwarta

Gwamnan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Lahadi, 12 ga watan Fabrairu ta hannun kakakinsa, Mamman Mohammed, ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mun karanta cike da damuwa rahotannin kafofin watsa labarai da ke yawo cewa an yi wa wasu masu ruwa da tsakin jam'iyyar ruwan duwatsu a wajen wani gangami a Gashua, jihar Yobe.
"Mun ga cewa akwai bukatar yin martani ga labarin na karya da ban tsoro don gudun batar da jama'a.
"Gangamin ya samu halartan mutane masu yawan gaske da ba'a taba ganin irinsu ba a tarihin siyasar garin Gashua.
"Dandazon jama'ar da suka taru sun fito don tarbar shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, Gwamna Buni da mambobin kwamitin yakin neman zaben.
"Gwamna Buni ya kutsa ta cikin dandazon mutanen cikin yanci yayin da magoya suka dunga jinjina masa yayin da ya isa zuwa kan mumbari.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: 'Yan Bindigan da Suka Yi Garkuwa da Kwamishina Sun Turo Sako Mai Ɗaga Hankali

"A lokacin da aka lura cewa mumbarin na fuskantar barazanar rushewa saboda dandazon jama'a, sai Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben APC, Sanata Muhammad Hassan, ya dakatar da duk wasu jawabai bayan na shugaban majalisar dattawan."

Mumbarin taron kamfen din APC a Gashua ya kusa rushewa saboda yawan jama'a

An tattaro cewa Hassan ya umurci kowa da ya sauka daga mumbarin saboda tsaro kafin ya rushe, inda aka ci gaba da raye-raye a wajen gangamin har sai da manyan mutanen suka tafi, ba a samu barkewar rikici ko wani abu ba.

An tattaro cewa bayan Gwamnan da mambobin kwamitin yakin neman zaben sun bar Gashua ne, sai sabani ya barke a tsakanin wasu kungiyoyin goyon bayansu biyu inda suka yi wa junansu barazana amma hakan bai kai ga an farmaki kowa ba.

Sanarwar ya kuma yi zargin cewa mawallafan labarin karyan na son nunawa duniya kamar babu jituwa tsakanin mutanen Gashua da APC a jihar Yobe ne.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Na San Yadda Zan Yadda Zan Gyara Tattalin Arzikin Najeriya, Bola Tinubu

Ni ne zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Atiku

A wani labari na daban, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP ya bugi kirjin cewa jam'iyyarsa ce za ta yi nasara a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel