Yaron Tsohon Gwamna ya Fito da Alherin da Tinubu Ya Yi wa Mahaifinsa da Aka Tsige Shi

Yaron Tsohon Gwamna ya Fito da Alherin da Tinubu Ya Yi wa Mahaifinsa da Aka Tsige Shi

  • Sanata Abdulaziz H. Nyako zai yi wa Asiwaju Bola Tinubu halaccin alherin da ya yi masu a 2014
  • Bayan an tunbuke Gwamna Murtala Haruna Nyako daga kan mulki, Bola Tinubu ya yi masa rana
  • Abdulaziz H. Nyako yana ganin yanzu lokaci ya yi da zai goyi bayan APC a zaben shugaban kasa

Abuja - Abdulaziz H. Nyako wanda ‘da ne a wajen Murtala Haruna Nyako, ya bude babin taimakon da Asiwaju Bola Tinubu ya yi wa mahaifinsa a baya.

Daily Trust ta rahoto Sanata Abdulaziz H. Nyako yana cewa ‘dan takaran shugaban kasar na APC ne ya taimakawa mahaifinsu a lokacin da aka tunbuke shi.

Sa’ilin yana Gwamnan jihar Adamawa a PDP, Murtala Haruna Nyako ya jagoranci wasu abokan aikinsa zuwa jam’iyyar APC, har ta kai aka tsige shi a 2014.

Kara karanta wannan

Wani Ya Shiga Katuwar Matsala a kan Zargin ‘Danuwan Buhari da Ganin Bayan Tinubu

Da yake amsa tambayoyi daga bakin ‘yan jarida a garin Yola, Sanata Nyako ya nuna cewa Bola Tinubu da Bukola Saraki ne suka ceci tsohon Gwamnan jihar.

Mutum biyu su ka ceci Nyako

Tsohon ‘dan majalisar yake cewa yana ganin darajar wadannan mutane biyu da suka tsayawa ubansu a yayin da har Gwamnonin Arewa suka yi watsi da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan siyasar yake cewa Tinubu da Saraki su ka san yadda suka yi, har Nyako ya fice daga Najeriya a daidai lokacin da jami’an tsaro ke neman yin ram da shi.

Tinubu
Bola Tinubu ana kamfe Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

“Asiwaju da Saraki suka taimakawa Admiral (Nyako) ya bar kasar nan. Yaron Asiwaju ne ya biya kudin masaukin Admiral (Nyako) a Landan.

- Abdulaziz H. Nyako

Nyako wanda ya wakilci Adamawa ta tsakiya tsakanin 2015 da 2019 ya shaida cewa hakan ta sa ya goyi bayan Saraki ya zama shugaban majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Tinubu Ya Jawo Hadimansa Suna Cin Mutuncin Shugaban kasa - Atiku

Ganin yadda tsohon Gwamnan na Kwara ya taimaka masu, Sanatan ya ce zai goyi bayan sa a kan Ahmad Lawan, sai dai idan Tinubu ne ya fito da kan shi.

Nyako yana tare da APC

An rahoto tsohon ‘dan takaran Gwamnan yana cewa zai marawa takarar Bola Tinubu baya a 2023. A zaben 2019, ya yi takara ne a karkashin jam'iyyar ADC.

‘Dan siyasar yake cewa ya zama dole ayi tikitin Musulmi da Musulmi a jam’iyyar APC domin a jawo hankalin Musulmai da domin ayi watsi da kiritsoci ba.

Buba Galadima ya fito da babban zargi

A rahoton da aka fitar dazu, an fahimci batun cewa akwai wadanda suka boye kudi gaskiya ne, Buba Galadima ya yarda da ikirarin gwamnatin tarayya.

Buba Galadima ya fito yana mai cewa ya san akwai wani Gwamna a Arewa maso yamma, wanda bayanan sirri sun tabbatar da yana da N22bn a gidansa.

Kara karanta wannan

Abin da Zai Faru Idan Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa a 2023 – Gwamnan APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel