Akwai Gwamna a Arewa da ya Boye Naira Biliyan 22 na Tsofaffin Kudi – Buba Galadima
- Buba Galadima ya yi ikirarin akwai Gwamnan Jihar da ya boye fiye da Naira Biliyan 22 a gidansa
- ‘Dan siyasar ya gaskata Gwamnatin Muhammadu Buhari na cewa wasu sun tanadi Biliyoyin kudi
- Injiniya Galadima yana ganin duk da haka zai fi kyau a hakura da canjin kudi saboda za ayi asara
FCT, Abuja - Buba Galadima ya fito yana zargin cewa an samu wani Gwamna a Najeriya wanda ya boye makudan tsofaffin takardun kudi.
A wata zantawa da ya yi da tashar talabijin Trust TV, Injiniya Buba Galadima ya shaida cewa wannan Gwamna ya boye Naira biliyan 22.
Jagoran na jam’iyyar adawa ta NNPP ya ce wannan Gwamna mai-ci yana mulki ne a wata jiha da ke yankin Arewa maso yammacin kasar nan.
A tattaunawar da aka yi da shi, ‘dan siyasar bai kama sunan wannan Gwamna ba, ko ya fadi jihar da yake mulki, ko akalla ya fadi jam’iyyarsa.
Buba Galadima ya nuna cewa ya yarda da gwamnatin Muhammadu Buhari da ta ke zargin akwai daidaikun mutanen da suka boye Nairori.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bayan sirri sun nuna Inji Buba
"Na san akwai Gwamna a Arewa maso yamma, wanda bayanan sirri sun tabbatar da yana da N22bn na tsofaffin kudi, ya boye su a cikin gidansa."
- Buba Galadima
Wannan bayani da ‘dan siyasar ya yi ta ba ‘dan jaridar mamaki, har ya nemi jin wani Gwamna ne haka, amma ‘dan siyasar ya ki fallasa shi.
“Ya san kan shi, kuma jami’an tsaro sun sani.”
- Buba Galadima
Da aka tambayi tsohon jigon na APC game da shirun da jami’an tsaro suka yi a kan batun idan zargin ya tabbata, sai ya ce watakila kare shi ne ake yi.
“Watakila su na tare da shi ne, ko kuma su na ba shi kariya. Tarkon da aka yi masa shi ne ya fita ya ce zai je ya canza wadannan kudi.
- Buba Galadima
Bai goyon bayan canjin kudi
Fitaccen ‘dan siyasar ya ce an samu Biliyoyin ne ta hanyar sata da rashin gaskiya a gwamnati. Jaridar Daily Post ta fitar da labarin a jiya.
Amma Injiniyan ya ce a maimakon wani talaka mai jarin N1000 a garin Yunusari a Yobe ya rasa jarin N1000, gara wancan mai kudi ya tsira.
A cewarsa, gara a bar tsarin ya cigaba da tafiya haka da talaka ya rasa abin da yake da shi.
Tasirin canjin kudi
Wani matashin ‘dan Jam’iyyar PDP a Kano, Adnan Mukhtar T/Wada ya shaida mana cewa farin jinin Atiku Abubakar da PDP ya karu sosai.
Hadimin na Shugaban masu yakin takarar Atiku Abubakar, Ibrahim Little ya ce tsarin canza kudi ya jawowa APC bakin jini a jihar Kano.
Asali: Legit.ng