Zargin Darektan Yakin Zaben Bola Tinubu a 2023, Ya Jefa Shi a Hannun Dakarun DSS

Zargin Darektan Yakin Zaben Bola Tinubu a 2023, Ya Jefa Shi a Hannun Dakarun DSS

  • Kamar yadda Atiku Abubakar ya nema, DSS sun gayyaci jigon APC da ya ce ana shirin juyin-mulki
  • Hukumar DSS masu fararen kaya su na neman Femi Fani-Kayode a dalilin bayana da ya fitar a Twitter
  • Darektan sashen harkar kafofin sadarwa na zamani a kwamitin yakin zaben APC zai amsa gayyatar

Abuja - Hukumar tsaro masu fararen kaya, DSS ta aikawa jagora a jam’iyyar APC mai mulki, Femi Fani-Kayode da goron gayyata kan kalaman da ya yi.

Daily Trust ta ce Femi Fani-Kayode ya bada sanarwar cewa jami’an DSS su na neman shi. ‘Dan siyasar ya yi wannan bayanin a wani jawabi a safiyar Litinin.

‘Dan siyasar wanda ya sauya-sheka daga PDP zuwa APC ya ce zai amsa gayyatar domin babu abin da yake tsoro, ya ce ba zai daina fadin ra’ayinsa ba.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Atiku Abubakar Ya Roki Jami’an Tsaro Su Cafke Tsohon Jigon PDP

“Kwanaki uku da suka wuce, a ranar da nayi magana a Twitter a kan rahotannin jaridu da ke zargin Atiku yana yin taro a boye da Sojoji.
Na samu sako daga wani mai ikirarin shi jami’in DSS ne, yana mai ba ni umarni in mika kai na gabansu da gaggawa saboda sha’anin tsaron kasa.
Nayi watsi da gayyatar domin ta bogi ce, saboda babu tabbacin cewa daga DSS sakon ya fito ban da niyyar zuwa ko ina sai an gayyace ni da kyau.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

'Yan DSS
Dakarun DSS Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Takarda ta fito daga DSS - FFK

Abin da ya ba ni mamaki, sai ga wasika daga wajensu, ana ba ni kwanaki biyu in bayyana a ofishinsu, an rubuto mani takardar jiya da yamma.
Sai na kira su a waya, sannan su ka nuna mani in dauki abin da muhimmanci, in gabatar da kai a lokacin da aka bada, ko abin ya iya yin muni.

Kara karanta wannan

Wani Ya Shiga Katuwar Matsala a kan Zargin ‘Danuwan Buhari da Ganin Bayan Tinubu

Tsohon Ministan harkokin jiragen saman ya ce akwai wani daga cikin karnukan farautar Alhaji Atiku Abubakar da aka ji yana kira ga jami’an DSS su cafke shi.

Ba don an tura masa da sako kwanaki biyu da suka wuce ba, Fani-Kayode ya ce da zai ce jami’an tsaron sun biyewa hadimin ‘dan takaran jam’iyyar hamayyar ne.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki

Cif Fani-Kayode ya yi amfani da wannan dama a Twitter ya soki takarar Atiku, yana cewa ba zai je ko ina ba, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai ci zabe.

A jawabinsa, ‘dan siyasar ya ce jami’an su na aikinsu ne yadda ya kamata, ya ce zai gabatar da kansa yadda aka bukata domin bai jin tsoron komai.

Ya kamata a cafke FFK - Atiku

Femi Fani-Kayode ya zargi Atiku Abubakar da hada-kai da wasu Janar domin a hana yin zabe, ya ce yanzu haka ana shirye-shiryen yin juyin mulki a kasar.

Kara karanta wannan

Sanatan APC Ya Fadi Wanda Zai Zama Babban Kalubale Wajen Shirya Zaben 2023

Bayan ganin maganganun Darektan kwamitin takaran APC, an ji labari Atiku Abubakar ya ce bai kamata ayi wasa da irin wadannan manyan zargi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel