Muna Mara Goyon Baya Ga Sauya Fasalin Naira: Majalisar Magabata

Muna Mara Goyon Baya Ga Sauya Fasalin Naira: Majalisar Magabata

  • An gama zaman majalisar magabatan Najeriya da aka fara tun da safiya a fadar shugaban kasa
  • Shugaba Muhammadu Buhari ne ya jagoranci wannan zama da aka kwashe tsawon lokaci ana yi
  • Jonathan, Obasanjo, Gowon, Abdus-Salam, da kimanin gwamnoni guda ashirin suka halarci zaman

Abuja - Majalisar magabata da masu ruwa da tsaki na tarayya ta ce tana goyon bayan gwamnatin tarayya da babban bakin Najeriya CBN kan kudirin sauya fasalin Naira.

Majalisar ta ce tana nuna goyon bayanta ne da sharadin bankin ya dau matakan gaggawa don tabbatar yan Najeriya sun samu isassun tsabar kudi a fadin kasa.

Sun bukaci gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya samar da isassun sabbin takardun Naira ko kuma ya fitar da tsaffi mutane suyi amfani, rahoton TheNation.

Council
Muna Mara Goyon Baya Ga Sauya Fasalin Naira Da Hana Amfani Da Tsaffi: Majalisar Magabata
Asali: Facebook

Antoni Janar na tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami tare da Gwamnan Legas Babajide Sanwoolu da Darius Ishaku na Taraba suka sanar da manema labaran fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Darakta Janar Na Kwamitin Kamfen Atiku Wuta

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malami ya ce abubuwa biyu aka tattauna a zaman; lamarin zaben 2023 da kuma lamarin sauya fasalin Naira.

A cewarsu, shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu da IGP na yan sanda, Alkali Baba, sun bada tabbacin cewa a shirye ake.

Game da lamarin Naira kuwa, an yi ittifakin cewa CBN ya tabbatar da ya buga isassun kudi domin share hawayen mutane.

Malamin yace:

"A karshe, abubuwa biyu aka yanke shawara kai a zaman majalisar. Na farko lamarin zabe kuma muna farin cikin da shirin da INEC da sauran hukumomi suka yi."
"Na biyu lamarin sauya fasalin Naira, ana tare da tsarin, amma majalisar ta ce wajibi ne bankin CBN ya tabbatar da an samar da isassun kudi ga jama'a."

Asali: Legit.ng

Online view pixel