Yanzu Yanzu: Gwamnatin Kano Ta Rufe Babban Kanti Kan Kin Karbar Tsoffin Naira

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Kano Ta Rufe Babban Kanti Kan Kin Karbar Tsoffin Naira

  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya yi umurnin rufe wani katafaren kantin siyayya a jihar
  • Hukumar kare hakkin masu siyan kayayyaki da masu siyarwa ta rufe kantin 'Wellcare' saboda kin karbar tsoffin takardun kudi daga wajen mazauna jihar
  • Gwamnatin jihar Kano ta gargadi yan kasuwa kan cewa za ta dauki tsattsauran mataki kan duk wanda ta kama yana kin karbar tsoffin kudi don bata haramta amfani da su ba

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta hannun Hukumar kare hakkin masu siyan kayayyaki da masu siyarwa ta rufe shahararriyar kantin nan mai suna Wellcare, kan kin karbar tsoffin takardun naira a ranar Lahadi, 12 ga watan Fabrairu.

A cewar mukaddashin shugaban hukumar, Baffa Babba Danagundi, an rufe kantin ne jim kadan bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umurnin, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Matasan APC sun yiwa Gwamna Mai Mala Buni rajamu a Yobe

Gwamna Abdullahi Ganduje
Yanzu Yanzu: Gwamnatin Kano Ta Rufe Babban Kanti Kan Kin Karbar Tsoffin Naira Hoto: @GovUmarGanduje
Asali: Twitter

Dalilin da yasa Ganduje ya rufe kantin Wellcare

Ya ce umurnin rufe kantin ya biyo bayan matakin da kantin Wellcare ya dauka na kin karbar tsoffin takardun Naira daga wajen kwastamomi wanda hakan ya saba umurnin da gwamnatin jihar ta bayar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Danagundi ya yi gargadi sauran yan kasuwa a Kano da su kwana da sanin cewa gwamnatin jihar bata haramta amfani da tsoffin Naira ba, don haka, duk shagon da aka kama yana kin karbar tsoffin kudin zai fuskanci mummunan hukunci.

Kantin da aka rufe ya nemi afuwa a wajen gwamnati

Jim kadan bayan rufe kantin 'Wellcare Alliance Limited' ya rubuta wasikar ban hakuri zuwa ga gwamnatin inda ya nemi a gaggauta shiga tsakani don sake bude kantin, rahoton The Cable.

Gwamnatin jihar Neja ta maka gwamnatin tarayya a kotu kan karancin Naira

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Gwamnatin Jihar Neja Ta Bi Takwarorinta Na Kogi, Kaduna Da Zamfara, Ta Maka Buhari a Gaban Kotu

A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnatin jihar Neja ta bi sahun takwarorinta na jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara wajen maka gwamnatin tarayya da babban bankin Najeriya a gaban kotu kan sabon manufar sauya kudi.

Gwamnatin Neja ta nemi a kara wa'adin daina karbar tsoffin kudi kamar yadda CBN ke shirin yi domin a cewarsa lokacin ya yi kadan da za a sauya su da sabbi wadanda suka yi karanci a kasar.

Ta ce hakan ya jefa al'umma cikin matsin rayuwa musamman mazauna karkara wanda hakan ya sa harkoki sun tsaya cak.

Asali: Legit.ng

Online view pixel