An Rasa Rai Yayin Da Magoya Bayan APC Da PDP Suka Yi Arangama A Jigawa

An Rasa Rai Yayin Da Magoya Bayan APC Da PDP Suka Yi Arangama A Jigawa

  • An rasa ran mutum guda sakamakon rikici da ya barke tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC da PDP a Maigatari a Jigawa
  • DSP Lawal Shiisu Adam, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Jigawa ya tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse
  • Adam ya ce rikicin ya faru ne yayin da magoya bayan PDP da suka tafi kamfen din dan takarar gwamna a Maigatari suka zo wuce wa ta gaban sakatariyar APC na garin

Jigawa - Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Jigawa ta tabbatar da kashe wani mutum daya sakamakon rikici da ya barke tsakanin mambobin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, da na yan jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a garin Maigatari, karamar hukumar Maigatari.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ne a Dutse, babban birnin jihar da mai magana da yawun yan sandan Jigawa, DSP Lawal Shiisu Adam ya fitar, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

2023: Dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar su Peter Obi ya kama hanyar Tinubu da Ganduje

PDP da APC
An Salwantar Da Rai Yayin Da Magoya Bayan APC Da PDP Suka Yi Arangama A Jigawa. Hoto: Channels TV
Asali: Twitter

Rundunar yan sanda ta bayyana yadda abin ya faru

Sanarwar ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"A ranar Juma'a 10 ga watan Fabrairun 2023 misalin karfe 6.30 na yamma, dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP ya tafi kamfe din sa a Maigatari.
"A yayin da suka isa sakatariyar APC, rikici ya barke tsakaninsu magoya bayan jam'iyyun biyu, kuma yan Santuraki Vanguard suka kai wa wani Abdullahi Isyaku dan shekara 35 mazaunin Gangare quarters hari a garin Maigatari."

Mai magana da yawun yan sandan ya ce:

"An garzaya da wanda abin ya faru da shi Babban Asibitin Gumel kuma daga baya ya rasu yayin da ake masa magani."

DSP Lawal Shi'isu Adam ya ce an kama mutane biyar da ake zargi da hannu a lamarin kuma ana cigaba da bincke a sashin binciken masu aikata manyan laifuka da ke hedkwatar rundunar yan sandan.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mataimakin Sufetan Yan Sanda Na Kasa, Lawan Jimeta, Ya Rasu, An Faɗi Abinda Ya Yi Ajalinsa

Lamarin ya haifar da fargaba da damuwa game da tsaron yan kasa da kuma yiwuwar kara tashin hankali a siyasar jihar, rahoton Channels TV.

Hukumomi sun yi kira ga dukkan jam'iyyun siyasa da su guji amfani da tashin hankali kuma su karfafa wa magoya bayansu gwiwa su rika harkokinsu cikin lumana.

Legit.ng Hausa ta samu tattaunawa da wani magoyin bayan jam'iyyar PDP mai suna Muhammadu Sani wanda ya yi karin haskekan lamarin.

Hayaniya ce irin ta magoya bayan siyasa duk da cewa yan takara suna iya kokarinsu na wayar da kan magoya bayansu su guji irin hakan.

Ya ce:

"Abin da ya faru bai kaddara ce kuma ina son in yi kira ga bangarorin biyu su rika kai zuciya nesa su yi siyasa ba da hayaniya ba, Allah ya jikan wanda ya riga mu gidan gaskiya."

Rikicin cikin gida ya raba kawunan yan jam'iyyar APC a Enugu

Kara karanta wannan

Tawagar Kamfen din Tinubu ta Fasa Gangamin da Zatayi a Kano, Bata Fallasa Dalili ba

A wani rahoton, kun ji cewa yiwuwan samun nasara ga jam'iyyar APC ya ragu sakamakon rikicin cikin gida da ya bulla a jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel