Mataimakin Sufetan Yan Sanda Na Kasa, Jimeta, Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Mataimakin Sufetan Yan Sanda Na Kasa, Jimeta, Ya Rigamu Gidan Gaskiya

  • Mataimakin Sufeta janar na yan sandan kasar nan mai kula da shiyya ta 5, AIG Jimeta, ya kwanta dama ranar Lahadi 12 ga watan Fabrairu
  • Mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya ce Jimeta ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Benin
  • Kafin rasuwarsa ya rike mukamai da dama a rundunar yan sanda daga bisani aka naɗa shi AIG a watan Janairu, 2022

Abuja - Mataimakin Sufeta janar na rundunar yan sandan kasar nan mai kula da shiyya ta 5 da ta kunshi jihohin Edo, Beyelsa da da Delta, Lawan Tanko Jimeta, ya rigamu gidan gaskiya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa AIG Jimeta ya rasu ne da safiyar ranar Lahadin nan a Asibitin koyarwa da ke Benin, babban birnin jihar Edo bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Matasan APC sun yiwa Gwamna Mai Mala Buni rajamu a Yobe

AIG Jimeta.
Mataimakin Sufetan Yan Sanda Na Kasa, Jimeta, Ya Rigamu Gidan Gaskiya Hoto: Police
Asali: UGC

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, ne ya tabbatar da rasuwar Jimeta a wata sanarwa da ya aike da ita ta dandalin Whatsapp ranar Lahadi, 12 ga watan Fabrairu, 2023.

A ruwayar Sahara Reporters, SP Wakil ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Inna Lillahi wa inna ilaihi raji’un, cikin karayar zuciya tare da miƙa lamari ga Allah mai girma da ɗaukaka, ina mai sanar da rasuwar A.I.G, Lawan Tanko Jimeta."
"Ya koma ga mahaliccinsa ne a Asibitin koyarwa da ke Benin, jihar Edo da safiyar nan (Lahadi) bayan fama da gajeruwar rashin lafiya. Daga Allah muke kuma gare shi wata rana zamu koma."
"Wannan shi ne karshen bawan Allah na gari, muna Addu'a Allah ya gafarta masa kura-kuransa kuma ya sa shi a gidan Aljannar Firdausy. Allah ya ba iyalansa karfin guiwar jure wannan rashi."

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji Sun Kashe Yan Ta'adda Da Dama, Sun Kwato Makamai A Kaduna

Legit.ng Hausa ta gano cewa marigayi AIG Jimeta ya karanci kwas din yaren Turanci a jami'ar Maiduguri a digirinsa na farko, kana ya wuce National Open University ya yi digiri na biyu.

Haka zalika an naɗa shi a matsayin AIG na Zone 5 a ranar 13 ga watan Janairu. 2022. Kafin nan ya rike mukamai da dama ciki har da kwamishinan 'yan sanda a Bauchi da Edo.

'Yan Sanda Sun Kama Makamai a Zamfara

A wani labarin kuma Jami'an hukumar 'yan sanda a Jihar Zamfara sun cafke mace da namiji ɗauke da daruɗuwan makamai

Jami'in huƙɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Muhammad Shehu, ya ce dubun mutanen ya cika ne a shingen binciken ababen hawa bayan samin bayanan siriii.

Tuni mutanen biyu suka masa laifinsu, sun ce suna sayarwa yan fashin jeji makamai a Zamfara da wasu jihohin maƙota.

Asali: Legit.ng

Online view pixel