Kwamitin Kamfen din APC na Shugaban Kasa ya Soke Yakin Neman Zabe a Kano

Kwamitin Kamfen din APC na Shugaban Kasa ya Soke Yakin Neman Zabe a Kano

  • Kungiyar magoya bayan Bola Tinubu ta sanar da soke zagayen kamfen din da zata yi ranar 16 ga watan Fabrairu a jihar Kano
  • Ta sanar da hakan ne a wata takarda da James Faleke ya fitar, wanda kungiyar ta wallafa
  • Kawo yanzu, Babu wanda yasan dalilin soke zagayen kamfen din, wanda sakataren kungiyar kuma 'dan majalisa ya rattaba hannu

Kano - Kungiyar kamfen din 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC ta soke zagayen da zatayi ranar 16 ga watan Fabrairu a jihar Kano.

Tutar APC
Kwamitin Kamfen din APC na Shugaban Kasa ya Soke Yakin Neman Zabe a Kano. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

James Faleke, 'dan majalisa kuma sakataren kungiyar ne ya sanar da haka ranar Alhamis, jaridar The Cable ta rahoto.

"Barkanku da yammaci. Ina sanar muku da soke zagayen da za mu yi a Kano na ranar 16 ga watan Fabrairu, 2023. Sa hannu. James Faleke."

Kara karanta wannan

Buhari a Sokoto: Tinubu ya Matukar Fahimtar Matsalolin Najeriya, Ku Zabe Shi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Kamar yadda kungiyar ta wallafa a shafinta na Twitter.

Sai dai, ba a sanar da dalilin sokewar ba.

Bola Tinubu, 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC ya je Kano ranar 4 ga watan Janairu don zagayen arewa maso yamma.

Shugaban PDP yayi barin zance, Yace PDP ta tafka abun kunya

A wani labari na daban, Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Dakta Iyorchia Ayu. yayi subul da baka yayin yakin gangamin zaben Atiku Abubakar, 'dan takarar shugabancin kasa na PDP a jihar Kano.

Ayu wanda ke gaban bainar jama'a yana kira garesu da su zabi Atiku, ya saki layi inda yace jam'iyyar PDP ta tafka abun kunya daga bisani kuma yace APC.

Ayu wanda yace APC bata tausayin talakawan Najeriya, ya sanar da cewa ya zama dole kada a zabe su idan ana son kawo daidato da canji a kasar nan.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Shiga Sabon Rudani, Mambobin PDP 8,000 Sun Koma APC a Arewa

Ba wannan bane karo na farko da 'yan takarkarin shugaban kasa ke yin subul da baka suna yabon manyan jam'iyyun adawa.

A jihar Filato, cikin watan Disamban da ya gabata, Bola Ahmed Tinubu, 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, ya ce Allah ya albarkaci jam'iyya P... daga bisanin ya kare da cewa jam'iyyar APC.

Wadannan abubuwan kuwa suna ja musu cece-kuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel