Abin Da Ya Sa Na Ki Karbar N150m Da Motar N80m Don In Bar Atiku, Naziru Sarkin Waka

Abin Da Ya Sa Na Ki Karbar N150m Da Motar N80m Don In Bar Atiku, Naziru Sarkin Waka

  • Shahararren mawakin Kannywood, Naziru Ahmad Sarkin Waka ya ce an masa tayin N180m da motar N80m don ya dena goyon bayan Atiku Abubakar a zaben 2023
  • Nazirun ya ce bai amsa kudin da motar ba saboda ya fifita masalahar kasa kan bukatar kansa don ya yi imanin Atiku zai fi Tinubu tabuka abin alheri
  • Ya kuma ce ko addinin musulunci ta koyar da cewa cikin halayen shugabanni na gari akwai lafiya da kwarin jiki wanda a cewarsa yana ganin Atikun ya fi Tinubu lafiya

Fitaccen jarumin Kannywood, Naziru Ahmad, da aka fi sani da Sarkin Waka ya yi ikirarin cewa an bashi Naira miliyan 150 da mota ta naira da miliyan 80 don ya yi watsi da dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, gabanin zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Wani Ya Shiga Katuwar Matsala a kan Zargin ‘Danuwan Buhari da Ganin Bayan Tinubu

Ahmad na daya cikin mawakan Hausa wadanda suka yi wa Atiku wakoki na kamfen kuma ya wasa a wurin ralli na jihohin arewa.

Naziru Ahmad
Abin Da Ya Sa Na Ki Karbar N150m Da Motar N80m Don In Bar Atiku, Naziru Sarkin Waka. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Shine ya yi shahararren wakar adawa da APC ta - 'APC Sai Mun Bata Wuta ...'

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mawakin na Kannywood kuma yana yi wa masu sarautar gargajiya waka a arewa kuma tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ne ya nada shi sarautar 'Sarkin Waka'

Da ya ke magana a wani shirin DW Hausa, mawakin na Kannywood ya ce ya ki amincewa ya yi watsi da Atiku don goyon bayan dan takarar shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Bola Tinubu.

Na yi imanin cewa Atiku ya fi Tinubu lafiya, Naziru

Jarumin na Kannywood ya ce ya yi imanin cewa Atiku ya fi Tinubu lafiya don haka zai fi shi tabuka abin azo a gani idan ya ci zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Darakta Janar Na Kwamitin Kamfen Atiku Wuta

Jaridar Leadership wacce ta bibiyi hirar ta ambato Ahmad yana cewa:

"Na fifita maslahar kasa fiye da bukatar kashin kai na.
"An bukaci in bar tafiyar Atiku domin wani dan takara kuma za a biya ni Naira miliyan 150 tare da mota ta Naira miliyan 80 amma ban karba ba.
"Na ki amincewa da tayin saboda na san Atiku zai yi shugabanci na gari kuma zai tsamo Najeriya daga mummunan halin da ta ke ciki.
"Ta yaya zan goyi bayan Tinubu wanda ba shi da lafiya da kwarin jiki? Addinin mu ya koyar da mu mu zabi masu lafiya a matsayin shugabanni don yana daya cikin halayen shugaba na gari."

Naziru ya yi wa Fati Slow da Ladin Cima babban kyauta

A wani rahoton kun ji cewa Naziru sarkin wakar ya gwangwaje Fati Slow da Ladin Cima da kyautar miliyoyin naira.

A cikin bidiyon da ya wallafa a Instagram, ya ce ya ba Ladi Cima kyautar ne don ta yi jari ta fara sana'a tana samun na abinci.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Tinubu Ya Jawo Hadimansa Suna Cin Mutuncin Shugaban kasa - Atiku

Asali: Legit.ng

Online view pixel