Canjin Kudi: Kwankwaso Ya Bayyana Matakin Da Zai Dauka Idan An Zabe Shi Shugaban Kasa

Canjin Kudi: Kwankwaso Ya Bayyana Matakin Da Zai Dauka Idan An Zabe Shi Shugaban Kasa

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP ya soki sauya fasalin naira da babban bankin kasa na Najeriya, CBN, ta yi
  • Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce CBN ta zabi lokaci da bai dace ba kuma ba ta yi tunani da tanade-tanaden da suka kamata ba kafin aiwatarwa
  • Kwankwaso ya yi alkawarin cewa zai tsawaita wa'adin canja kudin idan an zabe shi shugaban kasa don bawa talakawa isashen lokaci su canja kudin

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, a ranar Juma'a, ya bayyana tsarin sauya fasalin naira na CBN a matsayin kuskure da ba a yi tunani kansa sosai ba.

Ya bayyana cewa lokaci da aka zaba aiwatar da tsarin bai dace ba don ya kara jefa yan Najeriya cikin talauci, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Na San Yadda Zan Yadda Zan Gyara Tattalin Arzikin Najeriya, Bola Tinubu

Kwankwaso
Sauya Fasalin Takardun Naira Kuskure Ne, In Ji Kwankwaso. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Zan tsawaita wa'adin canja kudi idan an zabe ni shugaban kasa, Kwankwaso

Da ya ke magana a shirin 'The Verdict 2023' na Channels TV, tsohon gwamnan na Kano ya yi alkawarin tsawaita wa'adin dena karbar tsohon kudin har sai mutanen kasa sun canja kudinsu ba tare da matsala ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Ina tunanin dukkan batun (sauya fasalin naira) kuskure ne musamman lokacin da aka zabi aiwatarwa. Komai na da lokaci. Ba mu goyi bayan sauya nairan ba saboda a wannan muhimmin lokacin muna son zaman lafiya da cigaba saboda mutane su zabi wanda suke so cikin kwanciyar hankali."

Kwankwaso, ya yi waiwaye kan lokacin da gwamnatin sa ta aiwatar da shirin 'e-payment' a jihar Kano, ya ce akwai babban aiki da za a yi kafin a sauya tattalin arziki ta koma na zamani.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Babu Wani Dan Najeriya Mai Hankali Da Zai Zabi APC Ko PDP A 2023

Ya kara da cewa:

"Idan kana son kawo irin wannan tsarin, akwai ayyuka sosai da za ka yi a kasa. Na yi irin wannan a Kano, mun yi wa kananan bankuna 37 rajista don shirin fara biyan e-payment a Kano. Bai kamata ya zama kamar hukunta mutane bane, amma yadda gwamnati ta yi tamkar hukunta mutane ne.
"Mun dade muna kira a tsawaita wa'adin, daga baya sun kara kwana goma amma hakan ma ba zai kawo wani canji ba. Damuwar mu shine talaka."

Muna fata INEC ba za ta maimaita abin da ta yi a Kano a 2019 ba, Kwankwaso

Da aka masa tambaya ko ya gamsu da shirin aiki gabanin babban zaben, ya ce yana addu'a wannan karon hukumar ta kasance mai zaman kanta ba tare da bangarenci ba.

Ya ce:

"Muna fatan sun shirya amma muna da damuwa saboda abin da suka yi a Kano a 2019. Addu'armu shine wannan karon su yi abin da ya ke dai-dai."

Kara karanta wannan

Saraki Ya Magantu Kan Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Ya Fada Ma Yan Najeriya Abun da Za Su Yi Wa APC

A bangare guda Kwankwaso ya kuma soki hasashen da wasu ke yi kan wanda zai ci zaben shugaban kasa na 2023.

Sanatan na Kano ya ce hasashen ba gaskiya bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel