Zaben 2023: Na San Yadda Zan Yadda Zan Gyara Tattalin Arzikin Najeriya, Bola Tinubu

Zaben 2023: Na San Yadda Zan Yadda Zan Gyara Tattalin Arzikin Najeriya, Bola Tinubu

  • Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya ce ya san yadda zan gyara tattalin arzikin Najeriya
  • Tsohon gwamnan na jihar Legas ya furta hakan ne a Lokoja, babban birnin jihar Kogi a jawabinsa na yakin neman zabe
  • Tinubu ya yi alkawarin cewa zai farfado da masana'antu irinsu kamfanin karafa na Ajaokuta, samar da ayyuka da yashe rafin Neja

Jihar Kogi - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Asiwaju Bola Tinubu ya ce ya san yadda zai gyara tattalin arzikin Najeriya fiye da sauran yan takarar.

Daily Trust ta rahoto cewa ya furta hakan ne a ranar Laraba a Lokoja, babban birnin jihar Kogi, yayin kamfen dinsa na shugabancin kasa.

Bola Tinubu
Zaben 2023: Na San Yadda Zan Yadda Zan Gyara Tattalin Arzikin Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: @daily_trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Allah Na Dogara Da Shi Domin Nasara," Tinubu Ya Fada Wa Mahalarta Taron Ruwa Da Tsaki Na APC

Ya ce:

"Na san yadda zan yi shi. Ni ne kan gaba, na fi sauran yan takarar. Mutumin da ya san hanya. Mutumin da ya san yadda ake habaka kudi. Mutum mai cika alkawari."

Ya ce wasu na ta zargi a lokacin da ya yi magana kan wahalhalun da sabon tsarin sauya naira ya janyo wa yan Najeriya, yana mai cewa yanzu hukuncin kotun koli ta wanke shi.

Tinubu wanda tawagarsa ta kamfe ta dira a jihar misalin karfe 4 na yamma ya cigaba da cewa jihar na da albarkatun kasa, ya kuma ce zai sauya jihar zuwa babban birnin masana'antu a kasar.

Zan farfado da kamfanin karafa na Ajaokuta, Asiwaju Bola Tinubu

Tinubu ya ce zai farfado da kamfanin sarrafa karafa na Ajaokuta tare da yashe rafin Neja da inganta aikin noma da kirkirar aiki.

Gwamna Yahaya Bello ya lissafa alherin da Tinubu zai kawo Najeriya

A jawabinsa, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana dan takarar na APC a matsayin mutumin da ya samu karbuwa a wurare da yawa.

Kara karanta wannan

APC Ta Dage Kamfen Dinta Na Shugaban Kasa a Wata Jihar Kudu, Ta Fadi Dalili

Bello ya kara da cewa idan Tinubu ya zama shugaban kasa, 'za a samu ayyuka da yawa, kudi, da gine-gine da gyara kamfanin Ajaokuta. Za a magance rashin tsaro.'

Wadanda ba su son dimokradiyya ne ke son kawo rudani a Najeriya, Asiwaju Tinubu

A bangare guda, Asiwaju Bola Tinubu ya wasu mutanen wadanda ba su son dimokradiyya ne suke son kawo rudani a kasar ta hanyar janyo karancin man fetur da takardun naira.

Tinubun ya yi kira ga magoya bayansa da sauran yan Najeriya su kwantar da hankulansu, yana mai cewa abin zai wuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel