Siyasar Kano: Masoya Sun Hadawa Abba Gida-Gida Gudumuwar N510m a Awa 3

Siyasar Kano: Masoya Sun Hadawa Abba Gida-Gida Gudumuwar N510m a Awa 3

  • An shirya bikin karbar gudumuwar takara, Abba Kabir Yusuf ya samu taimakon N511, 257, 000
  • Abba Kabir Yusuf yana neman takaran Gwamnan jihar Kano a karkashin Jam’iyyar NNPP
  • ‘Yan siyasa, ‘yan kasuwa, magoya baya, masana da malaman makaranta sun bada gudumuwarsu

Kano - ‘Dan takaran Gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, ya samu gudumuwar makudan kudin yakin zabe daga jama’a.

A wani jawabi da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce magoya-baya da masoya sun tarawa Abba Kabir Yusuf N511, 257, 000 domin shirin zaben bana.

Kamar yadda Sanusi Bature Dawakin Tofa ya shaida a shafinsa na Facebook, kudin sun samu ne bayan yin bikin tara gudumuwar a ranar Lahadin da ta wuce.

Shugaban kwamitin tara gudumuwar jam’iyyar NNPP a Kano, Dr. Abdulrahman Kawu Sumaila ya karanto adadin wadannan miliyoyi kudi da aka tara.

Kara karanta wannan

Masu Tunanin Akwai Wani Sabani Tsakanina da Buhari Za Su Ji Kunya Inji Tinubu

Ina za a kai gudumuwar da aka samu?

Abdulrahman Kawu Sumaila yake cewa za ayi amfani da gudumuwar wajen kai-komon kamfe da zabe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake magana a Twitter, ‘dan takaran da aka fi sani da Abba Gida Gida, ya ji dadin ganin yadda Kanawa su ka rika aiko da kudinsu domin ganin nasararsa.

Siyasar Kano
Taron neman gudumuwar NNPP Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Tijjani Abdulkadir Jobe ya bada N50m

Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe mai wakiltar mazabar Dawakin Tofa, Rimingado da Tofa ne shugaban masu bada gudumuwa, kuma ya bada N50m a wajen.

Jawabin ya ce Dr. Abdulmumin Jibrin ya bada N20m yayin da Sani Muhammad Hotoro da Alhaji Nasiru Muhammad Danfaranshi kowa ya bada N20m.

Irinsu Hon. Kabiru Alhassan Rurum da Hon. Badamasi Ayuba sun bada gudumuwar N10m. 'Yan kasuwan waya da malaman makaranta sun bada kasonsu.

Legit.ng Hausa ta na da labari an samu gudumuwa daga Ali Madaki, Maliki Kuliya, Namadi Dala, Jamilu Ahmad, Wada AA Rano, Garba Hungu da sauransu.

Kara karanta wannan

Kamar Kananan Yara: Minista da Tsohon Shugaban Majalisa Sun Kaure da Cacar Baki

Kwankwaso ya je taron

Legit.ng Hausa ta fahimci ‘dan takaran shugaban kasa a NNPP kuma tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya halarci bikin neman gudumuwar.

A jawabin da ya yi, Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna kasar nan ta shiga mawuyacin halin da ta ke bukatar gwamnatin NNPP domin a nemawa al’umma mafita.

APC ta tsaida kamfe

A wata sanarwa da aka ji daga bakin Olawale Sadare, an fahimci Bola Tinubu ba zai je jihar Oyo ba, APC tace halin da ake ciki ya jawo aka dauki matakin nan.

Mai magana da yawun APC a Oyo ya ce za su karbi bakuncin Bola Tinubu, amma ba a yau ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel