Yobe Ta Arewa: Kotun Koli Ta Shirya Yanke Hukunci Kan Sahihin Dan Takarar APC Tsakanin Lawan Da Machina

Yobe Ta Arewa: Kotun Koli Ta Shirya Yanke Hukunci Kan Sahihin Dan Takarar APC Tsakanin Lawan Da Machina

  • Yan kwanaki kafin babban zaben kasar, kotun koli na shirin yanke hukunci kan shari'ar Machina da Sanata Ahmad Lawan
  • A yau Litinin, 6 ga watan Fabrairu ne kotun mai kololuwar hukunci a Najeriya za ta tabbatar da sahihin dan takarar sanata mai wakiltan Yobe ta arewa a karkashin APC
  • Jam'iyyar APC mai mulki ce ta kalubalanci hukuncin kotun daukaka kara da ya tabbatar da Machina a matsayin dan takararta inda ta dage cewa Lawan ne wanda ta zaba

Yobe - Kotun koli ta shirya zartar da hukunci a kan rikici da ya barke kan tikitin takarar kujerar sanata mai wakiltan Yobe ta Arewa karkashin inuwar jam'iyyar ll Progressives Congress (APC) a yau Litinin, 6 ga watan Fabrairu .

Jam'iyyar APC na kalubalantar zaben Bashir Machina a matsayin dan takarar jam'iyyar a yankin Yobe ta arewa, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kungiyar PDP Ta Roki Yan Najeriya Da Su Zabi Atiku Saboda Dalili Daya

Lawan da Machina
Yobe Ta Arewa: Kotun Koli Ta Shirya Yanke Hukunci Kan Sahihin Dan Takarar APC Tsakanin Lawan Da Machina Hoto: Ahmed Lawan, Bashir Sheriff Machina
Asali: Facebook

Jam'iyyar ta dage cewa Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya, shine sahihin dan takararta a yankin Yobe ta arewa a zabe mai zuwa.

Yadda zaman karshe ya gudana a kotun daukaka kara

A zaman karshe da aka yi a kotun daukaka kara, lauyan jam'iyyar, Sepiribo Peters, ya yi mahawara cewa zaben fidda gwanin da aka yi a ranar 28 ga watan Mayun shekarar bara wanda ya samar da Machina ya saba dokar zabe ta 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Peters ya bayyana cewa wani Danjuma Manga ne ya gudanar da zaben fidda gwanin da ake magana a kai kuma ba kwamitin aiki na jam'iyyar bane ya zabe shi.

Ya sanar da kotun cewa APC ta soke zaben fidda gwanin kan hujjar saba ka'ida da aka yi a lokacin zaben.

Ya yi korafin cewa kwamitin NWC ne ya gudanar da daya zaben fidda gwanin da aka yi a ranar 9 ga watan Yuni, kuma ya samar da Lawan a matsayin sahihin dan takarar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Zance ya kare, kotu ta fadi wanda zai yi takarar gwamna a PDP a jihar Taraba

A kori karar APC saboda bai da inganci, lauyan Machina ga kotun koli

Sai dai kuma, lauyan Machina, ya roki kotun koli da ta yi watsi da karar da aka daukaka kan rashin inganci bisa hujjar cewa shugaban majalisar dattawan bai kalubalanci shari'ar ba a kotunan kasa biyu.

Ya kuma bayyana cewa Manga wanda ya gudanar da zaben fidda gwanin da Machina ya ci, ya kasance mamba a kwamitin NWC wanda aka nada don gudanar da shirin.

APC ta tunkari kotun daukaka kara a Abuja tana neman a soke shari'ar kotun kasa da ya ayyana Machina a matsayin dan takarar APC a yankin Yobe ta Arewa.

Sai dai kuma shugabar kotun, Justis Monica Dongban-Mensem wacce ta jagoranci shari'ar ta riki cewa karar da aka daukaka cin mutuncin tsarin kotu ne.

Kwamitin mutum biyar na babban kotun kasar karkashin jagorancin Justis Centus Nweze ne ya tsayar da yau Litinin, 6 ga watan Fabrairu domin yanke hukunci kan shari’ar, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Kallabi: Laila Buhari ta banke namiji a kotu, ta lashe tikitin sanatan mazaba a jihar Kano

Hadimin Tambuwal ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

A wani labarin, hadimin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwa, Abubakar Kwaire, ya raba gari da shi inda ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Kwaire ya samu kyakkyawar tarba daga dan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Sokoto, Ahmad Aliyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel