El-Rufai: Buhari Sai Da Ya Kadu Da Ya Ji Labarin Ahmad Lawan Ne Zababben Dan Takarar Shugaban Kasa Na APC

El-Rufai: Buhari Sai Da Ya Kadu Da Ya Ji Labarin Ahmad Lawan Ne Zababben Dan Takarar Shugaban Kasa Na APC

  • Yan kwanaki kafin zaben shugaban kasa na 2023, Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana yadda suka yi da Shugaba Buhari kan wanda APC za ta tsayar don ya gaje shi
  • El-Rufai ya ce Buhari ya kadu sosai a lokacin da ya ji cewa Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa jam'iyya mai mulki ta tsayar a matsayin dan takarar maslaha
  • Gwamnan na Kaduna ya ce nan take shugaban kasar ya fada masu cewa sam bai san da wannan zancen ba babu yawunsa a ciki

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kadu matuka lokacin da aka sanar masa cewa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ake so a tsayar a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Da yake jawabi yayin amsa tambayoyi a wani shirin TVC a ranar Alhamis, 2 ga watan Fabrairu, El-rufai ya ce shugaban kasar bai da masaniya kan zabar Lawan da aka yi.

Kara karanta wannan

Na Rantse Ba Wanda Muke Tsoro A Kasar Nan, El-Rufa'i Ya Mayarwa Fulogan Buhari Martani

Buhari da Lawan
El-Rufai: Buhari Sai Da Ya Kadu Da Ya Ji Labarin Ahmad Lawan Ne Zababben Dan Takarar Shugaban Kasa Na APC Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

A cikin watan Yunin 2022, yan awanni kafin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Adamu, ya sanar da shugaban majalisar dattawa a matsayin dan takarar maslaha.

Wannan sanarwar ta haddasa cece-kuce inda mutane da dama suka yi adawa da shi a wancan lokacin ciki kuwa harda gwamnonin APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya ce ba da yawunsa aka tsayar da Ahmad Lawan ba

Da yake jawabi, El-Rufai ya ce Buhari ya fito fili ya bayyana matsayinsa kan wanda yake so ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, rahoton The Cable.

Daily Post ta nakalto El-Rufai yana cewa:

"Muma mun ji haka. Mambobin kwamitin aiki na kasa sun kira mu sannan suka bayyana cewa shugaban jam';iyyar na kasa ya fada masu cewa shugaban majalisar dattawa ne dan takarar maslaha.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

"Kuma, gwamnonin APC na arewa sun nemi ganawa da shugaban kasa. Mun je ga shugaban kasa sannan muka ce ya shugaban kasa, ga abun da muke ji, Ba abun da kake ta fada mana ba kenan a shekaru biyu zuwa uku da suka shige. Shin da gaske ne hakan?
"Kuma shugaban kasar ya nuna kaduwa sannan ya ce 'bana daga cikin wannan'. Kuma nan take a wancan lokaci, ya sammaci Garba Shehu don fitar da sanarwar cewa bai da dan kowani dan takara da yake so. Kuma ya fada mana karara 'ba ni da kowani dan takara da nake so."

A wani labari na daban, mun ji cewa kungoyoyin magoya bayan Shettima/Tinubu sun bi gida-gida don tallata yan takarar na APC a jihar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel