Dattawan Arewa Sun Aikawa Shugaban Kasa Buhari Muhimmin Sako a Kan Shirin Zabe
- Kungiyar NEC ta Dattawan Arewacin Najeriya ta aiko sakon gargadi ga Muhammadu Buhari
- Tanko Yakasai ya fitar da jawabi cewa akwai na kusa da shugaban kasa da ke yin amfani da shi
- Ganin zaben 2023 ya gabato, Dattawan sun nuna ba za su goyi bayan abin da zai iya jawo rigima ba
Abuja - Northern Elders Council (NEC) wanda kungiya ce ta Dattawan Arewacin Najeriya ta yi kira na musamman ga shugaba Muhammadu Buhari.
Daily Trust ta rahoto cewa Kungiyar NEC ta ja-kunnen Mai girma shugaban Najeriyan da ya tabbatar da an zayi zabe na adalci da gaskiya a bana.
Tanko Yakasai wanda yake jagorantar kungiyar ya ankarar da Muhammadu Buhari a kan wasu marasa rike da mukamai da ke cin karensu babu babbaka.
Dattijon ya yi gargadi cewa wadannan mutane da ke juya gwamnati su na kokarin amfani da kusancinsu da shugaban kasa wajen hargitsa shirin zabe.
Na zagaye da Buhari sun sa son-rai
A cewar Tanko Yakasai, na-kusa da shugaba Buhari na amfani da damarsu saboda son rai. Rahoton bai kama sunayen na kusa da shugaban kasar ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan bayani ya fito a wani jawabin da kungiyar NEC tayi inda ta jaddada cewa tana goyon bayan abin da zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.
“Har kullum, Kungiyar NEC ba za ta fasa kokarin da take yi na wanzar da zaman lafiya, hadin-kai da kwanciyar hankali a Najeriya.”
- Tanko Yakasai
A jawabin da aka fitar a garin Abuja, NEC a karkashin jagorancin Tanko Yakassai ta ce tana sa ido a kan abubuwan da ke faruwa a harkar siyasar kasa.
Dattijon mai shekara 97 yake cewa za su hada-kai da sauran masu sha’awar cigaban kasar nan domin ganin ba a samu wata matsala a wajen zabe ba.
Ba za mu kula Nasir El-Rufai ba
Ana haka sai aka ji Hakeem Baba-Ahmed ya yi magana a shafin Facebook dangane da wasu kalamai da aka ji daga bakin Gwamna Nasir El-Rufai.
Dr. Hakeem Baba-Ahmed wanda shi ne Sakataren yada labarai na kungiyar NEF ta Dattawan Arewacin Najeriya ya ce ba za su biyewa El-Rufai ba.
“Wadanda suke jira mu mayar wa Gwamna El-Rufai martani sai kuyi hakuri. Dattijo baya halin tir.
Alhamdulillah, duk dan Arewa na kirki ya san Arewa na da dattawa daga iyaye har masu mata hankoro.Allah Ya tsare mu, Ya shirya El-Rufai."
Yakubu Dogara v Festus Keyamo
An ji labari tsohon shugaban majalisar tarayya, Yakubu Dogara ya soki goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu da shugaban kasa yake yi a zaben bana.
Sannan Hon. Yakubu Dogara ya yi kaca-kaca da Festus Keyamo da cewa bai taba cin zabe a tarihi ba, bayan Ministan ya soke matsayar da ya dauka.
Asali: Legit.ng