Tinubu Zai Yi Aikin Kawo Sauyi, Zai Tafi da Matasa, Inji El-Rufai

Tinubu Zai Yi Aikin Kawo Sauyi, Zai Tafi da Matasa, Inji El-Rufai

  • Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana kalan shugabancin da Bola Tinubu zai yi idan ya gaji Buhari a zaben bana
  • Gwamnan na APC ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka yi dashi a ranar Laraba 1 ga watan Fabrairun 2023
  • El-Rufai ya ce, Tinubu zai zama shugaban da zai dama da matasa a mulkinsa, don ya yi kira da su mai da hankali su zabe shi

Gabanin zaben 2023 na shugaban kasa, gwamnan APC, El-Rufai ya bayyana cewa, babu wani aiki a gwamnati da matasa ba zasu iya yi ba, kuma Tinubu zai dama da matasa a mulkinsa.

A fahimtarsa, idan aka zabi Tinubu, za a yi shugaban da zai zama raba gardama da zai kawo sauyi mai yawa ga kasar nan.

Kara karanta wannan

2023: Wasu Masu Son Gaje Buhari Abin Dariya Ne, Gwamnan Arewa Ya Tabo 'Yan Takarar Shugaban Kasa

A cewarsa, da yawan ‘yan takarar shugaban kasa a zaben mai zuwa da suka haura shekaru 70 sun fito ne domin yiwa matasa shawar fage don gane abin da suke bukata.

Tinubu zai kawo sauyi, inji El-Rufai
Tinubu Zai Yi Aikin Kawo Sauyi, Zai Tafi da Matasa, Inji El-Rufai | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Wadannan batutuwa na El-Rufai na fitowa ne a lokacin da yake tattauna da gidan talabijin na Channels da safiyar ranar Laraba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zan ba Tinubu shawarin ya dama da matasa idan ya gaji Buhari

Ya kuma shaida cewa, zai ba Tinubu shawarin irin matasan da ya kamata ya zaba ya yi tafiya dasu idan yana bukata a gwamnatinsa.

A cewarsa:

“Bana tunanin akwai wani aiki na gwamnati da ba za a iya ba matashi ba. Kamar yadda na fada, har yanzu muna magana.
“Fasfon Najeriya shi kadai ne fasfo da nake dashi. Duk abin da zan yi don ganin kasa ta ta yi kyau, zan yi kokari na yi. Amma kamar yadda nake fada kullum na fi son gani a kasa.”

Kara karanta wannan

Wahalar Naira Da Mai: Akwai Wasu Na Kusa Da Buhari Da Basu Son Tinubu Yaci Zabe, El-Rufa'i

Irin shugaban da za a yi idan Tinubu ya gaji Buhari

Ya kara da cewa, Bola Ahmad Tinubu zai dama da matasa a gwamnatinsa da za ta zama mai motsi kuma mai kawo sauyi.

A kalamansa:

“Yana da wahala ga dan shekara 40 ko 50 ya iya gamsar da Najeriya ko kuma ‘yan siyasa cewa yana da gogewar kula da wannan kasar mai sarkakiya. Ina daukar ‘yan sama da shekaru 70 da suke neman takara a matsayin shugabannin wucin gadi.”

El-Rufai na daga cikin gwamnonin Arewa da ke bayyana goyon bayansu ga tafiyar Bola Ahmad Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel