Fadar Shugaban Kasa ta Magantu Kan Ikirarin El-Rufai na Makiyan Tinubu a Aso Villa

Fadar Shugaban Kasa ta Magantu Kan Ikirarin El-Rufai na Makiyan Tinubu a Aso Villa

  • Ministan yada labarai, Lai Mohammed, yace hankalin Buhari ya karkata wurin ganin an yi zaben gaskiya ba zagon kasa ga wani 'dan takara ba
  • Lai Mohammed ya musanta ikirarin Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna inda yace akwai tantama kan batun zagon kasa ga wani 'dan takara da Villa
  • Yayi wannan martanin ne bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya inda yake amsa tambayoyi daga manema labaran gidan gwamnati

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya tayi martani kan zargin Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna kan wasu da ke fadar Shugaban kasa da ke zagon kasa ga 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC.

Gwamna El-Rufai yayi wannan ikirarin ne yayin da ya bayyana shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.

Buhari da malam
Fadar Shugaban Kasa ta Magantu Kan Ikirarin El-Rufai na Makiyan Tinubu a Aso Villa. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Ministan yada labarai, Lai Mohammed, yayi martani yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya wacce Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a yau.

Kara karanta wannan

Gwamna Masari Ya Tattauna Da Buhari Kan Zaben Gwamnan Jihar Katsina

Mohammed ya jaddada matsayar shugaban kasan kan cewa mulkinsa zai mayar da hankali ne wurin tabbatar da an yi zaben gaskiya ba tare da an ja wa wani faduwa ba, jaridar Punch ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da yin tantamar cewa idan akwai wani da ke aikin zagon kasa ga kowanne 'dan takara, toh gaskiya ba asan shi ba a hukumance, Channels TV ta rahoto.

A yayin tambayoyi da amsoshinsu, ministan yada labarai ya kara da martani kan sakamakon da Transparency International ta saki na ranar Talata.

Ya bayyana cewa hukumomin EFCC da ICPC suna da tarihi maus kyau na nasarori don haka wannan sakamakon gwamnati bata damu da shi.

Ya bayyana cewa, yaki da mulkin nan yake da rashawa ba wai don ta kayatar da Transparency Internation bane amma don ta kawo cigaba ga kasa a fannin siyasa da tattalin arziki ne.

Kara karanta wannan

A Karon Farko, Peter Obi Ya Magantu Bayan Tinubu Ya Ci Zabe, Ya Yi Alkawarin Abu 1 Tak

'Yan bindiga sun hari caji ofishi da ofishin INEC, sun halaka mutum 1

A wani labari na daban, wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari caji ofis da ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a Idemili da ke jihar Anambra.

An gano cewa, sun jefa abubuwa masu fashewa ne yayin da suka budewa mazauna yankin wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel