Ba Zai Je Ko Ina Ba: El-Rufai Ya Bayyana Inda Peter Obi Zai Kare a Takarar 2023

Ba Zai Je Ko Ina Ba: El-Rufai Ya Bayyana Inda Peter Obi Zai Kare a Takarar 2023

  • Gwamnan jihar Kaduna ya yi hasashen jihohin da Peter Obi zai samu a zaben shugaban kasa
  • Malam Nasir El-Rufai ya ce a bangaren kudancin kasar nan kurum LP za ta iya samun kuri’u
  • A ra’ayin El-Rufai, zaben bana zai kasance tsakanin Atiku Abubakar da Bola Tinubu ne kurum

Abuja - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yana ganin cewa babu ta yadda Peter Obi zai lashe zabe mai zuwa, ya zama shugaban kasar Najeriya.

Mai girma Gwamnan ya zanta da gidan talabijin nan na TVC, inda ya nuna cewa ‘dan takaran jam’iyyar LP ba zai iya yin nasara a zabe mai zuwa ba.

Tsohon Ministan ya misalta ‘dan takaran kujerar shugaban kasar da ‘dan wasan kwaikwayon Nollywood wanda ba zai samu kuri’un da ake so ba.

A ra’ayin Nasir El-Rufai, kuri’un Peter Obi za su fito ne daga yankinsa na Kudu maso gabas da kuma wasu jihohin da ke kudu maso kudancin kasar.

Kara karanta wannan

Na Rantse Ba Wanda Muke Tsoro A Kasar Nan, El-Rufa'i Ya Mayarwa Fulogan Buhari Martani

The Cable ta rahoto Malam El-Rufai yana mai cewa Obi da jam’iyyarsa ta LP ba za su samu kuri’u a Arewa maso gabas ko a Arewa maso yamma ba.

Peter Obi
Peter Obi a Kebbi Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mu ne a kan gaba - El-Rufai

"Mu ne a gaba. Ta ina Peter Obi zai lashe wani zabe? Peter Obi zai samu 1% ne a Sokoto, 2% a Katsina, 5% a Kano. A nan kuri’u suke, jihohi ba daya ba ne.
Saboda ka samu 70% na kuri’un Anambra bai nufin wanda ya kawo 10% na kuri’un Kano bai fi ka kokari. A Kano ana maganar samun kuri’u miliyan hudu ne.
Kuri’un da suke Anambra shi ne na wata karamar hukumar Kaduna, jihohin ba daya ba ne.
Idan ka tattara kuri’un Jihohi ka ce sun zama daya, kwarai Peter Obi zai karbe jihohin Kudu maso gabas, zai yi kokari a Kudu maso Kudu; to, sai kuma ina?

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan Jam’iyyar APC Yana Kara Fitowa Baro-Baro Daf da Zaben 2023

Ba zai tabuka abin kirki a Kudu maso yamma ba, kuri’unsa ba za su wuce tamkar allura a teku a Legas ba. Yana tattara kuri’un Kiristocin Arewa da kyau.
Amma su nawa ne? Obi ba zai iya lashe zaben nan ba. Bai da adadin jihohin da ake so; bai da 25% - da na duba bai wuce ya samu kuri’a a jihohi 16 kurum ba.”

- Nasir El-Rufai

An rahoto Gwamnan yana cewa zaben bana tsakanin jam’iyyun APC da PDP ne, ya ce nuna kabilanci da amfani da addinin Peter Obi ba zai iya kai LP ko ina ba.

NNPP ba za ta janye takara ba

Injiniya Buba Galadima ya ce ba a banza suke shiga daji da sako-sako ba, yake cewa Rabiu Kwankwaso takara ya fito yi a zaben 2023 ba da wasa ba.

An fahimci wannan ne yayin da Buba Galadima yake maida martani a kan wasu kalamai da ake cewa Atiku Abubakar yafada da aka yi hira da shi.

Kara karanta wannan

Raba gardama: El-Rufai ya fadi abin da Tinubu ya tsara yi idan ya gaji Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel