Muna Magana da Su – Atiku Ya Kyankyasa Yiwuwar Haduwa da Kwankwaso ko Obi

Muna Magana da Su – Atiku Ya Kyankyasa Yiwuwar Haduwa da Kwankwaso ko Obi

  • Atiku Abubakar ya nuna bai jin tsoron haduwa da Asiwaju Bola Tinubu ko wani ‘dan takara a siyasa
  • ‘Dan takaran kujerar shugaban kasar ya ce babu mamaki PDP ta hada-kai da LP ko NNPP a 2023
  • Wazirin Adamawa ya ce jam’iyyar PDP za ta doke Tinubu domin kowa ya gaji da Gwamnatin APC

Abuja - A wata hira ta musamman da aka yi da shi a gidan BBC Hausa, ‘dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya tattauna kan batutuwa iri-iri.

Atiku Abubakar ya nuna cewa shakka babu PDP ta na fama da kalubale kamar kowace jam’iyyar siyasa a dalilin sabaninsa da Gwamnonin G5.

Duk da rikicin cikin gidan jam’iyyar hamayyar, Alhaji Atiku Abubakar ya ce wannan ba zai hana shi samun nasara wajen zama shugaban Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Wani hanzari: Sirri ya fito, tsohon kakakin majalisa ya ce hadari ne a ba Tinubu ragamar Najeriya

‘Dan takaran yake cewa zabe ya canza a Najeriya saboda dokokin da aka fito da su, saboda haka yake cewa gwamnonin G5 ba za su iya murde zabe ba.

Zabe ba tabbas, sai an tashi kurum - Atiku

Da aka tambayi Wazirin Adamawa a game da bangarewar da Atiku Abubakar da Peter Obi suka yi daga PDP, ya nuna sam hakan bai tada masa hankali.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A tattaunawarsa da gidan talabijin, babban ‘dan siyasar ya ce ko da ‘yan takaran LP da NNPP su na PDP har gobe, babu tabbacin zai lashe zabe mai zuwa.

Atiku
Atiku Abubakar a taron kamfe Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Duk da zabe ya karaso, tsohon Mataimakin shugaban kasar ya shaida cewa yana tattaunawa da wani a cikin Kwankwaso ko Obi da nufin su hada-kai.

Kwarin gwiwar PDP a 2023

A game da tunkarar Bola Tinubu, Atiku ya ce bai jin ‘dan takaran APC ya san lagonsa a siyasa.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu: Yadda Nayi Ta Lallabar Buhari, Har Aka Kara Wa’adin Canza Tsohon Kudi

Babban abin da ke ba Atiku Abubakar kwarin gwiwar jam’iyyar PDP za ta karbe mulki shi ne gwamnatin APC ta gaza, a cewarsa kowa yana neman canji.

"Gwamnatin APC ta gaza, kowa ya sani ta gaza ta kowane fanni. Mutane su na son canji."

- Atiku Abubakar

An yi wa ‘dan takaran jam’iyyar hamayyar tambaya a game da zargin rashin gaskiya, sai ya ce babu hujjojin da za su gaskata laifin da ake tuhumar da shi.

Rikicin cikin gidan PDP

A baya an samu rahoto cewa Atiku Abubakar da abokin gaminsa, Ifeanyi Okowa sun ziyarci jihar Kebbi domin yakin neman zaben shugaban kasa a PDP.

Wasu ‘yan jam’iyyar hamayyar a Kebbi ba su je tarbar Atiku ko su halarci yawon kamfe da ya zo ba, amma duk da haka an ga jiga-jigan 'yan siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel