'Yan Kwankwasiyya Sun Kona Jar Hula, Sun Koma Bayan Tinubu a Zaben 2023

'Yan Kwankwasiyya Sun Kona Jar Hula, Sun Koma Bayan Tinubu a Zaben 2023

  • Magoya bayan Kwankwaso da ake kira 'yan Kwankwasiyya sun kona jar hula a Kano ranar Lahadi
  • Mutanen suna cikin mambobin siyasa 10,000 daga PDP, NNPP, ADC da wasu jam'iyyu waɗanda suka sauya sheka zuwa APC
  • Kwankwaso na neman zama shugaban ƙasa a inuwar NNPP mai kayan marmari a zaben 25 ga watan Fabrairu

Kano - Tsoffin magoya bayan ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, sun ƙona jar hula da aka saba ganin tsohon gwamna na saka wa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa mutanen sun kuma ayyana cikakken goyon bayansu ga ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Yan Kwankwasiyya.
'Yan Kwankwasiyya Sun Kona Jar Hula, Sun Koma Bayan Tinubu a Zaben 2023 Hoto: thenation
Asali: UGC

Tsoffin 'yan Kwankwasiyya na cikin mutane 10,000 da suka fice daga jam'iyyun PDP, NNPP, ADC da wasu jam'iyyu suka koma jam'iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hukumar Yan Sanda Ta Kama 'Yar TikTok, Murja Kunya A Kano

Mutanen sun samu kyakkyawar tarba hannu bibbiyu daga ƙungiyar magoya bayan Tinubu, 'USIR North West Project For Tinubu/Shettima 2023' ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabar ƙungiyar, Haiiya Umma Salma Isyaku Rabiu, ta ce:

"Yau mun taru anan ne domin maraba da murna da waɗan nan mambobi 10,000 waɗanda suka ga ya dace su tattara kayansu daga jam'iyyunsu su dawo cikin APC."
"Dukkansu suna da katin zama mambobin jam'iyyun PDP, NNPP, ADC, PRP, ADP da wasu jam'iyyun siyasa, sun yanke shawarin ficewa daga duhu zuwa haske, daga koma baya zuwa ci gaba."
"Kamar yadda kuke gani waɗan nan mutanen sun zo nan ne saboda haɗin kai da cigaban APC a matsayin jam'iyya ɗaya tilo da bata da tsara a Najeriya."
"Jam'iyyar da take kishin mutane, jam'iyyar da take son ci gaba da gina Najeriya zuwa mataki na gaba, jam'iyyar da take ƙaunar Najeriya da 'yan Najeriya."

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyun Siyasa 40 Sun Yanke Shawara, Sun Fadi Wanda Zasu Marawa Baya Tsakanin Atiku da Tinubu

Ta kuma bayyana cewa masu sauya shekar sun fara tunanin ɗaukar matakin shiga APC tun bayan da aka ayyana Tinubu a mataayin ɗan takarar da ya lashe zaben fidda gwani.

Hajiya Umma Salma ta yi shaguɓe ga sauran masu neman kujera lamba ɗaya a Najeriya inda aka ji tana iƙirarin Bola Tinubu ne kaɗai a cikin tseren gaje Buhari, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kwankwaso Bai Da Kwarewar Mulkin Najeriya, Tsohon Sakataren NNPP

A wani labarin kuma Tsohon Jigon NNPP ya ce Kwankwaso da jam'iyyarsa ba zasu kai labari ba a zaɓen watan Fabrairi

Dakta Babayo Liman, tsohon sakataren NNPP na shiyyar arewa maso gabas ya tona abinda ke wakana na rashin tsarin cin zaɓe a jam'iyyar Kwankwaso.

Ya ce ya yanke shawarin sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP ne saboda ya tallafa wa, Atiku Abubakar , ya lashe zaben shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan Daba Sun Kai Hari Kan Ayarin Ɗan Takarar Gwamnan PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel