Hukumar Yan Sanda Ta Kama 'Yar TikTok, Murja Kunya A Kano

Hukumar Yan Sanda Ta Kama 'Yar TikTok, Murja Kunya A Kano

  • A daidai lokacin da take shirin murna da biki mai armashi, yan sanda sun cika hannu da Murja Kunya
  • Rahotanni sun bayyana cewa an damke Murja ne a dakin Otal a cikin birnin jihar Kano
  • Murja Ibrahim ta kasance mai watsa bidiyoyi a manhajar sada zumunta ta TikTok kuma tana da dimbin mabiya

Jami'an hukumar yan sandan Najeriya shiyyar jihar Kano sun cika hannu da shahrarriyar mai yin bidiyon barkwancin a shafin TikTok Murja Ibrahim Kunya.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa an damketa ne a dakin Otal na Tahir.

An damketa tana kokarin kama dakuna wa baokanta da ke shirin zuwa Kano halartan bikin zagoyowar ranar haihuwarta.

Zaku tuna cewa a shekarar 2022, kotun Shair'a ta bukaci kwamishanan yan sandna jihar ya damke Murya Kunya tare da sauran yan TikTok bisa laifin gurbata tarbiyya al'umma.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Gano Gawar Mutane 10 a Jihar Kaduna, Gwamnati Ta Sa Dokar Kulle a Garuruwa 4

Murja
Hukumar Yan Sanda Ta Kama 'Yar TikTok, Murja Kunya A Kano
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran yan TikTok da umurci a kama sun hada da Mr 442, Safara’u, Dan Maraya, Amude Booth, Kawu Dan Sarki, Ado Gwanja, Ummi Shakira, Samha Inuwa da Babiana.

Rundunar ƴan sandan Kano ta ce, ta kama Murja Ibrahim Kunya bayan ƙorafin da Zauren Malaman Kano suka yi a kanta da wasu masu amfani da TikTok.

Wata majiya ta ƙara da cewa tuni manyan mutane suka shiga sahun neman a saki Murjan.

Mawaƙin TikTok da Hisbah

Kwanakin baya, hukumar hisba ta kama wani mawaƙi waishi Al-Amin G-Fresh akan wasa da sallah a cikin bidiyon sa na TikTok, rahoton MI3 Novels.

Bayan wa'azi da tunatarwa, mawaƙin ya amsa laifin sa kuma ya tuba nan take.

Duk da dai ba'a hukunta shi ba, Hisba ta tauna tsakuwa don aya taji tsoro ta hanyar yi masa aikin malu, sannan tabashi shawarar ya koma islamiyya wanda ya yarda zai koma.

Kara karanta wannan

Kotu ta Daure Jagororin Jam’iyyar PDP a Kurkuku a Dalilin Cin N140m Saboda Murde Zabe

Gargadin hukuma NCC game da TikTok

A watan Disamba 2022, Hukumar Sadarwa ta Najeriya ta gargadi 'yan Najeriya kan hadarin shiga sabuwar gasar Tik-Tok mai suna "Invisible Challenge" tana mai cewa hakan kan iya sawa wayoyinka bairos, rahoton Premium Times.

Tace wannan gasar na baiwa wasu damar shigar da bairos din cikin na'o'urorin da kuke amfani da ita, inda su ringa sa ma bairso din daga kwamfuwutar su inji NCC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel