Bola Tinubu Ya Yi Magana a Kan ‘Kama’ Wasu Tirelolin Tsofaffin Kudi 8 Daga Gidansa

Bola Tinubu Ya Yi Magana a Kan ‘Kama’ Wasu Tirelolin Tsofaffin Kudi 8 Daga Gidansa

  • Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya ce labarin cafke wasu motocin tsofaffon kudi daga gidansa ba gaskiya
  • ‘Dan takaran ya karyata wannan ta bakin mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai
  • Bola Ahmed Tinubu ya zargi ‘yan adawar da siyasa da kitsa masa sharri, ya nemi ayi watsi da jita-jitar

Abuja - Mai taimakawa Asiwaju Ahmed Bola Tinubu wajen harkokin yada labarai, Malam Abdulaziz Abdulaziz ya fitar da sabuwar sanarwa a wani jawabi.

A daren Lahadi, hadimin Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya fito shafin Facebook, yana mai karyata wasu labaran bogi da suke ta yawo a kofofin sadarwa na zamani.

Akwai wasu gidajen yada labarai (ban da Legit.ng Hausa) da suka rika yada cewa an damke wasu manyan motoci dauke da makudan tsofaffin kudi za a kai banki.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'Sight and Sounds' Ta Shirya Taro Kan Manufofin Asiwaju Bola Tinubu

Masu yada wannan labari da ‘dan jaridar ya kira da na bogi, suna ikirarin ‘dan takaran shugaban kasa a APC, Ahmed Bola Tinubu ya mallaki wadannan kudi.

Tsantsagwaron karya ce kurum

A sanarwar da ya fitar, Mai taimakawa ‘dan takaran shugaban kasar ya ce zunzurtun karya ake yi wa mai gidansa, an kitsa labarin ne kurum saboda bata masa suna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Abdulaziz Abdulaziz ya ankarar da jama’a idan aka lura rahotannin ba su da wani tushe ko makama, saboda haka ya fadawa mutane su yi watsi da labarin.

Bola Tinubu
Marafa, Matawalle, Tinubu a Zamfara Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Hadimin ‘dan takaran na jam’iyya mai mulki yake cewa ganin aski ya zo gaban goshi a yakin neman zabe, lallai za ayi ta samu ‘yan adawan da ke da bakar aniya.

Abdulaziz a jawabinsa ya kara da cewa masu fito da irin wadannan labarai na karya, ba za su iya doke ‘dan takaran a filin zabe ba ne, shiyasa suka hada da yin sharri.

Kara karanta wannan

Ban Yi Nufin Tsanantawa Talakawa Da Lamarin Sauya Fasalin Naira Ba: Buhari

‘Dan takaran ya jaddada cewa bai goyon bayan yin sharri da sunan siyasa, a kyale mutane da zabi. Premium Times Hausa ta fitar da labarin nan a ranar Asabar.

Cikakken jawabin Abdulaziz Abdulaziz

“Mun lura da wasu shafukan labarai na bogi musamman a Facebook suna yaɗa wani labarin ƙarya da yarfe irin na siyasa wanda suke rawaito cewa wai an kama wasu motoci da kuɗaɗe mallaki ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC.
Wannan magana ƙarya ce tsagwaronta wanda maƙiya suka shirya domin domin bata sunan Alhaji Ahmed Bola Tinubu. Abin lura a nan shi ne babu wata madogara da su waɗannan masu yaɗa labarun ƙarya suka dogara da ita wajen rawaito wannan magana ta bogi.
Muna Jan hankali mutane da su lura da cewa a kwanakin da suka rage mana kafin shiga zaɓe ƴan siyasa marasa tsoron Allah da dama za su yi ta Ƙoƙarin yaɗa labaran ƙarya da sharri domin ɓata sunan abokan hamayyar su da suke ganin cewa ba za su iya kayarda da su a akwatin zaɓe ba sai sun haɗa da ƙarya da sharri domin ɓata musu suna.

Kara karanta wannan

Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma, Daga Dr Sani Rijiyar Lemo

Ɗan takarar jam'iyyar APC, Jabagan Borgu ya sha faɗar cewa shi bai yarda da yin sharri ko yarfen siyasa ba domin ba sahihiyar hanya ce ta cin zaɓe ba. Abinda muka dogara da shi shi ne a bar mutane su yi zaɓin ɗan takarar da suka ga ya dace kuma yana da ƙwarewar aiki da zai iya kawowa ƙasa cigaba, ba tare da an bi haramtaciyyar hanya ba wajen ru&ar da tunanin masu zaɓe.
Muna kira ga jama'a da su yi watsi da wannan labarin bogi marar hujja wanda wasu maƙiya kuma marasa son zaman lafiya zuka ƙirƙira."

- Abdulaziz Abdulaziz

Kwankwaso ya yi Allah-wadai da CBN

Wani rahoto ya zo cewa masu kuɗi su ajiye kudinsu, idan Rabiu Kwankwaso ya zama shugaban kasa, zai canza masu duk da tsarin da CBN ya shigo da shi.

Kwankwaso mai neman takara, ya ce mutane su ajiye kudinsu da PVC, idan suka zabi jam'iyyar NNPP, dukiyarsu zata dawo salin-alin ba tare da wahala ba.

Kara karanta wannan

Kamfe Ya Tsaya Babu Shiri Bayan An Kora ‘Yar Takarar M/Gwamna da Ta je Yakin zabe

Asali: Legit.ng

Online view pixel