Canjin Kudi: Kwankwaso Ya Yi Alkwarin Gyara ‘Kuskuren’ da Aka Yi Idan Ya Ci Zabe

Canjin Kudi: Kwankwaso Ya Yi Alkwarin Gyara ‘Kuskuren’ da Aka Yi Idan Ya Ci Zabe

  • Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi Allah-wadai da tsarin da aka kawo na sauya wasu manyan takardun Nairori
  • Injiniya Rabiu Kwankwanso ya nuna mutane musamman a karkara su na shan wahalar wannan tsarin
  • Ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP ya ba gwamnati da CBN shawarar a tsawaita wa’adin canjin

Abuja - Rabi'u Musa Kwankwaso mai neman mulkin Najeriya a jam'iyyar NNPP, ya nuna rashin goyon bayansa a kan canjin manyan takardun Naira.

Rabi'u Musa Kwankwaso ya zanta da BBC Hausa, inda ya shaida mata zai fi kyau Gwamnan babban bankin CBN ya kara wa’adin amsar tsohon kudi.

‘Dan takaran shugaban kasar yake cewa Bayin Allah sun shiga kunci saboda tsarin da aka fito da shi bayan buga sababbin kudi, a ra’ayinsa kuskure ne.

An rahoto Rabiu Kwankwaso yana mai cewa idan ya lashe zabe mai zuwa, ya kuma zama shugaban Najeriya, zai canzawa duk masu kudi, dukiyarsu.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Kai Ziyarar Bazata Kudancin Borno, Ya Kafa Tarihi

Shawara ga Gwamnatin Buhari

An hirar da aka yi da shi ‘Dan takarar kujerar shugabancin kasar ya nuna damuwarsa a kan yadda aka fito da tsarin kwatsam a kurarrren lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A matsayinsa na ‘dan adawa, Kwankwaso ya ce abin da za su iya shi ne ba gwamnati shawara cewa akwai bukatar la’akari da halin da talaka yake ciki a yau.

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso a Karshi Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Da a ce NNPP ta ke rike da mulkin Najeriya, Kwankwaso ya nuna da ba zai taba goyon bayan a canza kudi a gabar nan ba, ya ce a karshe talaka ya wahala.

Mutane za su rasa dukiyoyinsu

A wata hirar dabam da aka yi da shi a gidan talabijin Arise, tsohon Gwamnan na Kano ya jaddada cewa mutanen karkara ba za su iya cin ma wa’adin CBN ba.

‘Dan siyasar ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tsawaita wa’adin, ya ce muddin ba ayi haka ba, mutane da-dama za su yi asarar tarin dukiyar da suka adana.

Kara karanta wannan

Ya fasa kwai: Tinubu ya fadi makarkashin yin sabbin Naira da karancin mai a Najeriya

Wani rahoto ya ce Kwankwaso ya saurari bayanan gwamnati, kuma a karshe duk ya fahimci an yi kuskure wajen bijiro da tsarinmusamman ta fuskar lokaci.

A ra’ayin ‘dan takaran, da wahala dokar tayi aiki a kan manyan ‘yan siyasa domin ‘yan jam’iyyun APC da PDP su ke da bankuna, kuma su na da Gwamnoni.

N370bn ba N89tr - CBN

A wani karin haske da aka yi a makon nan, kun ji labari bankin CBN ya ce tun daga shekarar 2016 zuwa yanzu, harajin da bankuna suka karba N370.686b ne.

Gwamnan babban bankin Najeriya ya karyata batun boye N89tr da Gudaji Kazaure yake yi. Godwin Emefiele ya ce a cikin kudin ragowar N144bn ne a CBN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel