Tinubu Bai Zagi Buhari Ba, PDP Da Yan jarida Ke Kokarin Hada su Rigima: APC

Tinubu Bai Zagi Buhari Ba, PDP Da Yan jarida Ke Kokarin Hada su Rigima: APC

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Nigeria ta zargi Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa na PDP da hada baki wajen karancin man fetir da kuma kudade
  • Daga cikin wanda jam'iyyar din ta zarga akwai wasu masu sharhi a jaridun Nigeria, wanda tace sune suke taimakawa
  • Jam'iyyar tace sune suka hada kanwa uwar gamin da suke taimakawa wajen yin karancin man da kuma sabbin kudi

Abuja - Jam'iyyar APC, bisa karkashin kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar APC ta ce jam'iyyar adawa ta PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar na kokarin hada fada tsakanin dan takarar jam'iyyarta da kuma fadar shugaban kasa.

Kwamitin kuma, ya zargi yan adawar da zabar wasu masu sharhi a jaridun Nigeria guda biyar dan rura wutar rikicin rashin mai da kuma karancin sabbin kudi a hannun mutane.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Kai Ziyarar Bazata Kudancin Borno, Ya Kafa Tarihi

Kwamitin yace yan adawa sun canja maganar da Tinubu yayi na kishin kasa kan man fetir da karancin sabbin kudi a jihar Ogun,

Ta ce kage ne da kazafi da kuma juya maganar akayi. Rahoton The Nation.

Atiku
PDP Da Wasu Masu Rubutu A Shafin Jaridu Sun Hada Baki Kan Karncin Mai Da Kuma Karancin Sabbin Kudi Hoto: The Nation
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata takarda da daraktan sadarwa da jama'a na kwamitin, Bayo Onuanuga ya sanyawa hannu a ranar Alhamis din nan, yace kwamitin yakin neman zaben atiku da jam'iyyarsa sun juyawa Tinubun magana ne, sabida su hada shi da Buhari.

Sanarwar tace wannan maganar ta Tinubu ta na nufin:

"Yayi kawai maganar ne dan nuna yadda gwamnati ta maida hankali kan yadda wasu suke kokarin zambatar kasar kan aiyukan mai da kuma sakewa kudi fasali, shi yasa jam'iyyar PDP, tai amfani da wannan abun ta canjawa Tinubun magana"

Karancin Kudi

Kara karanta wannan

Yan Daba A Jihar Lagos Sun Kaiwa Dan Takarar Gwamnan Jihar Lagos Hari yayin Da Yake Kamfe

An sha ji daga wajen manyan jami'an bankin kasa ciki harda gwamnan bankin na karyata karancin kudi a hannun mutane, inda suke cewa sun ringa sun wadata bankunan da kudaden.

A yan kwanan nan bankuna sun rufe injunan cirar kudi yayin da suka taikaita wanda suke bada sabbin kudin, sannan wasu bankunan har yanzu suna bada tsoffin kudin, inji rahotan The Nation

Hadi kawai ake so ayi

Kwamitin yakin neman zaben Tinubun yace kawai so ake a hadasu da shugaba Buhari sabida sunka Tinubun ya dau hanyar nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel