Zaben 2023: Tinubu Ya San Cewa Atiku Ne Zai Zama Shugaban Kasa, In Ji Shu'aibu

Zaben 2023: Tinubu Ya San Cewa Atiku Ne Zai Zama Shugaban Kasa, In Ji Shu'aibu

  • Phrank Shaibu, daya daga cikin mataikan Atiku ya bayyana cewa Tinubu ya karaya tun kafin aje ko ina
  • Ya nuna yadda Tinubu yake magana kamar shine a jam'iyyar adawa saboda yasan Atiku ne shugaban kasa
  • Phrank ya bayyana cewa kodai rudewa ko kuma Tinubu ya riga yasan Atiku ne zai lashe zaben 2023

Phrank Shu'aibu, mataimaki na musamman ga dan takarar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa dan takarar APC, Bola Ahmed Tinubu, yasan cewa Atiku ne zai lashe zaben shugaban kasa na 2023, Daily Trust ta rahoto.

Shuaibu ya bayyana haka a shirin gidan talabijin na Channels TV siyasa a yau.

Phrank Shuaibu
Tinubu Yasan Atiku Ne Zai Zama Shugaban Kasa, In Ji Prank Shu'aibu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu ya sha zargin PDP da kawo wahalar mai ga yan kasa don bata sunan gwamnati saboda dalilai na siyasa.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zabe, Tinubu Ya Daukarwa Iyaye Gagarumin Alkawari Da Zai Cika Masu a Kan 'Ya'yansu

Dan takarar na APC a wani taron yakin neman zabe a Abeokuta, Jihar Ogun, ya bayyana cewa za su sauya fasalin abubuwa a kasar nan.

Tinubu yana magana kaman shine ke jam'iyyar adawa, Shu'aibu

Da ya ke martani akan batutuwan biyu, Shaibu ya ce;

''Bai kamata Tinubu ya dinga kamfen kamar shine a jam'iyyar adawa ba. A wajen wa zai karbi mulki? Ko Jiya (Laraba) sai da ya ce zamu karbi mulki a hannunsu kai kace Atiku Abubakar ne shugaban kasa.
''Sun fitar da sanarwa cewa karancin mai da kuma tsarin takaita takurdun kudi tsarukkan Atiku ne. Ministan mai shine babban kwamanda kuma shugaban kasar Najeriya. Wannan shine Shugaba Muhammadu Buhari."

Ya cigaba da cewa:

"Gwamnan babban bankin kasa CBN ya samu umarni daga Muhammadu Buhari kuma a gwamnatin APC. To in har dan takarar wata jam'iyya zai bayyana cewa zaiyi juyin juya hali, ya kamata hukumar DSS su dau abin da muhimmanci. Tinubu ba shi da rigar kariya. Ya kamata a kama shi kuma a bincike shi.

Kara karanta wannan

Tinubu Na Da Tunani Irin Na Sarakunan Kama Karya, Naja'atu Ta Tono Bakin Shafin Dan Takarar APC

''Bazai yi wu ka dinga maganar juyin juya hali saura kwanaki 29 zabe kuma idan har ya fadi zabe, irin wannan mutumin ba zai yarda da faduwa ba kuma zai tayar da hargitsi duba da yadda ya kafa kungiyar magoya bayan Jagaban.
''Kodai yana fama da gigin tsufa ko kuma ya riga yasan Atiku ne shugaban kasa. A zuciyarsa yasan Atiku ne zai zama shugaban kasa".

Asali: Legit.ng

Online view pixel