Kamfe Ya Tsaya Babu Shiri Bayan An Kora ‘Yar Takarar M/Gwamna da Ta je Yakin zabe
- Funke Akindele ta ziyarci kasuwar kayan marmari da ke Ikosi domin tayi wa jam’iyyar PDP kamfe
- ‘Yan daba sun aukawa, ‘Yar wasar mai neman zama mataimakiyar gwamnar jihar Legas a zaben 2023
- Kakakin Jam’iyyar hamayya ta PDP a Legas ya ce ba kowa ya kitsa wannan aiki ba sai Abolanle Bada
Lagos - Funke Akindele mai neman zama mataimakiyar gwamnar jihar Legas a jam’iyyar PDP ta ji babu dadi a wajen wani yawon kamfe da ta je.
Vanguard ta fitar da labari cewa wasu ‘yan banga da dabar siyasa sun kora Funke Akindele a lokacin da ta shiga kasuwar kayan marmari a Ikosi.
A ranar Talata, 25 ga watan Junairu 2023 lamarin ya faru da ‘yar wasan kwaikwayon da ta tsaya neman kujerar mataimakiyar gwamnan 2023 a PDP.
Da hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta zanta da ‘dan takaran Gwamnan Legas a inuwar PDP, Abdul-Azeez Adediran ya tabbatar da hakan.
Hakan ya faru - Jandor
Abdul-Azeez Adediran wanda aka fi sani da Jandor ya ce abin da ya faru ya takaita masu yawon kamfe da suka je yi a wannan kasuwa da ke Legas.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da ya hadu da babban limamin masallacin Ketu, Jandor ya shaida masa an dabawa wani jami’in tsaronsu wuka, sannan aka raunata wasu ‘yan jarida.
‘Dan takaran ya ce hakan ya sa Akindele ta hakura da yawon kamfe da aka fito, su kuma sauran ‘yan tawagar su ka cigaba da yakin neman zabensu.
Martanin jam’iyyar PDP
Mai magana da yawun bakin jam’iyyar PDP ta reshen jihar Legas, Hakeem Amode ya fadawa Premium Times cewa an tura masu gungun ‘yan daba ne.
Hakeem Amode yake cewa sun saba shiga kasuwanni domin tallata jam’iyyar adawa ta PDP ga mata masu kasuwanci, a Ikosi sai aka ci karo da miyagu.
Jam’iyyar PDP ta na zargin shugabar karamar hukumar Ikosi, Abolanle Bada ta kawo ‘yan daba a kasuwar, su ka auka masu saboda su na neman kuri’u.
A Oktoban 2022, Jandor ya koka da an kai masu hari da suka shiga wasu wurare yin kamfe. Amode ya ce sun saba da ganin barazana cikin kasuwanni.
Mubaya'ar Coalition of United Political Parties
An ji labari kungiyar CUPP ta ji dadin yadda Atiku Abubakar yake goyon bayan a canza fasalin kasa, kuma ya yi alkawarin zai karawa jihohi karfi.
Sannan ganin Atiku ya yi mataimakin shugaban kasa kuma ya dauko Kiristan Kudu, Gwamna Ifeanyi Okowa, CUPP ta ce shi za ta marawa baya a 2023.
Asali: Legit.ng