Har Yau Banga Sabbin Kudi Ba, Gwamnan PDP Ortom Ya Nemi Buhari Ya Kara Wa’adin Daina Karbar Tsohon Kudi

Har Yau Banga Sabbin Kudi Ba, Gwamnan PDP Ortom Ya Nemi Buhari Ya Kara Wa’adin Daina Karbar Tsohon Kudi

  • Gwamnan jihar Benue ya ce bai taba ganin kudin da CBN ta buga a kwanakin nan ba, ya nemi mafita
  • Gwamna Samuel Ortom ya roki shugaba Buhari da ya duba tare da sauraran koken 'yan Najeriya, 'yan kasarsa
  • Ya bukaci a dage wa'adin daina amfani da tsoffin kudade zuwa wani lokaci daban don ba 'yan Najeriya dama mai da kudade

Makurdi, jihar Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue a ranar Laraba 25 Janairu, 2023 ya ce har yanzu bai sa idonsa a kan sabbin Naira ba.

Orom ya bayyana hakan ne yayin wani taron da aka yi a jami’ar Joseph Sarwuan Tarka ta noma a birnin Makurdi ta jihar, Tribune Online ta ruwaito.

Ya kuma bayyana cewa, ya kamata CBN ya saurari kiran da ‘yan Najeriya ke yi tare da kara wa’adin daina amfani da stoffin kudi.

Kara karanta wannan

Da walakin: CBN ya yi sabon batu game da karancin sabbin Naira da aka buga kwanan nan

Ortom ya ce bai taba ganin sabbin Naira ba
Har Yau Banga Sabbin Kudi Ba, Gwamnan PDP Ortom Ya Nemi Buhari Ya Kara Wa’adin Daina Karbar Tsohon Kudi | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Idan baku manta ba, babban bankin Najeriya ya ce ba zai kara wa’adin daina kashe tsoffin kudi ba a kasar, inda yace akwai sabbi kowa ya karba a bankunan kasuwanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar Talata, majalisar dokokin Najeriya ta yi kira ga CBN da ya duba tare da kara wa’adin zuwa karshen Yulin bana.

Wa'adin CBN zai taba zukatan 'yan Najeriya

Ortom ya ce, tsayuwa kan wa’adin na CBN zai jawowa ‘yan kasar koma baya da kuma cutar dasu ba gaira babu dalili, Daily Post ta tattaro.

A cewarsa:

“Abin da ya bayyana shine akwai mutane da yawa musamman a kauyuka da ke bukatar shigar tsoffin kudi. A matsayina na gwamna, har yanzu ban ga sabbin kudin ba.
“Wannan ne dalilin da yasa nake tare da sauran ‘yan Najeriya a wannan yanayi mai kunci don ganin lamarin bai yi muni ga mutanenmu ba.

Kara karanta wannan

Ndume: Sanatan da Bai Taba Rike Sababbin N200, N500 da N1000 da CBN Ya Buga ba

“Abu ne da za a gane cewa mutanenmu a Najeriya na shan wahala. Mutane na tafiya da kunci a kasar nan abubuwa ba daidai suke ba ko ta ina. Ina kira ga shugaban kasa da ya duba tare da kara wa’adin."

A tun farko, babban bankin Najeriya ya ce babu gudu babu ja da baya, ba zai kara kwana daya ba kan wa'adin da ya dauka na daina amfani da tsoffin kudi.

Don haka ne ma ya shawarci 'yan Najeriya da su daina karbar tsoffin kudade daga bankuna idan aka basu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel