An Fashe Ta Murna Yayin Da Kotun Koli Ta Bada Hukunci Na Karshe Akan Dan Takarar Gwamna A PDP

An Fashe Ta Murna Yayin Da Kotun Koli Ta Bada Hukunci Na Karshe Akan Dan Takarar Gwamna A PDP

  • Kotun koli ta yi watsi da daukaka kara da aka yi kan PDP da dan takarar gwamnanta a jihar Ogun, Oladipupo Adetutu
  • Jimi Lawal, daya cikin yan takarar gwamna da wasu daliget na mazabu ne suka daukaka karar a kotu
  • Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun, yayin karonto hukuncin da tawagar alkalai biyar suka yanke, ta ce wanda ya shigar da karar bai da hurumin kallubalantar zaben cikin gidan

Bisa alamu rikicin da ake yi a kotu a jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya zo karshe a yayin da kotun daukaka kara ta yi watsi da daukaka kara 4 kan tikitin takarar na jam'iyya.

Kotun daukaka karar ta yi watsi da karar da Jimi Lawal, daya cikin masu neman takarar gwamna a jam'iyyar da wasu daliget, tana mai cewa ba su da hurumin kallubalantar zaben fidda gwanin, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jam'iyyar APC Ta Yi Martani Kan Yunkurin Da PDP Ta Yi Na Haramtawa Tinubu Takara

Ogun PDP
An Fashe Ta Murna Yayin Da Kotun Koli Ta Bada Hukunci Na Karshe Akan Dan Takarar Gwamna A PDP. Hoto: PDP Update
Asali: Facebook

Alkalan kotun, yayin hukuncin da suka yi tarayya a kai sun tabbatar da Oladipupo Adebutu a matsayin halastaccen dan takarar gwamna na PDP a babban zaben na 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An warware rikicin PDP na jihar Ogun?

Alkalai 5 karkashin jagorancin Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun ne suka bada hukuncin bayan lauyoyin masu kara sun janye.

An yi fatali da karar na Tayo Olabode, daya cikin wadanda suka daukaka karar kan PDP da dan takarar gwamna, Oladipupo Adebutu, kan cewa ba dai hurumin shigar da karar.

Alkalan sun yarda cewa daliget din da ke ikirarin cewa an tauye musu hakkin kada kuri'ansu yayin zaben cikin gida na PDP ba su da ikon kai wanda ya lashe zabe da jam'iyyar kara a kotu, saboda su ba yan takara bane.

Abin da ke faruwa a baya-bayan nan game da PDP, Jihar Ogun, Ladi Adebutu, zaben 2023

Kara karanta wannan

Yadda Atiku Abubakar Zai Bi Wajen Dankara Tinubu da Peter Obi da Kasa Inji PDP PCC

Kotun daukaka karar ta ce, wadanda suka yi takara a zaben fidda gwanin ne kadai ke da hurumin kallubalantar sakamakon zaben fidda gwanin ba sauran mambobin jam'iyya ba.

An kuma yi watsi da wata karar saboda rashin aikawa wanda ake tuhuma sammaci, kotun ta ce wanda ake tuhumar ya shiga lamarin daga farko har karshe.

Zaben 2023: Tinubu Ya Yi Taro Da Malaman A Jihar Bauchi

A wani rahoto, Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya yi taro da malaman addinin musulunci na arewa maso yamma a gabanin zaben 2023.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya yi alkawarin yin adalci ga kowa idan an zabe shi shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel