Zaben 2023: Jam'iyyar APC Ta Yi Martani Kan Yunkurin Da PDP Ta Yi Na Haramtawa Tinubu Takara

Zaben 2023: Jam'iyyar APC Ta Yi Martani Kan Yunkurin Da PDP Ta Yi Na Haramtawa Tinubu Takara

  • A yayin da babban zaben shekarar 2023 ke karatowa, ana cigaba da hayaniya a tsakanin jam'iyyun siyasa da yan takara
  • Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki a Najeriya na musayar maganganu da jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP
  • A baya-bayan nan, PDP ta shigar da kara a kotu na neman hana Bola Tinubu takara a matsayin dan takarar shugaban kasa na APC a zaben 2023

Biyo bayan karar da jam'iyyar PDP ta shigar a babban kotun tarayya na neman haramtawa Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa yin takara, kan zargin safarar miyagun kwayoyi, kwamitin kamfen din shugaban kasa ta yi martani.

A martanin da ta yi, kakakin kwamitin kamfen din na APC, Festus Keyamo (SAN) ya ce PDP ba ta da gaskiya.

Ahmed Bola Tinubu
Zaben 2023: Jam'iyyar APC Ta Yi Martani Kan Yunkurin Da PDP Ta Yi Na Haramtawa Tinubu Takara. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cewar Vanguard, ya ce:

Kara karanta wannan

Tinubu Musulmin Boge Ne, Yan Arewa Ba Zasu Zabeshi Ba: PDP

"Me yasa suka tsaya tsawon watanni har sai da muka shigar da kara sannan suka garzaya kotu? Na kallubalance su fiye da wata biyu da suka shude, amma ba su yi komai ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Hakan na nuna tawaga wacce ba ta da asali, babu hangen nesa da basira. Kawai dai son shigar da kara kishiyar namu suke son yi.
"Amma yan Najeriya sun gane halinsu; Masu tallata SPV suna kokarin wasa da hankulan mutane. Yan Najeriya sun yanke hukunci. Yan Najeriya sun juya musu baya."

Kazalika, direktan watsa labarai na kamfen din APC, Bayo Onanuga ya kalubalanci dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya yi magana kan SPV da aka alakanta da shi.

Maganan SPV din wani shiri ne na yaudara da tsohon hadimin Atiku Michael Achimugu ya tona ya saki wani murya na magana da tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi da ke bayyana cewa a kafa SPV din ne don karkatar da kudade zuwa asusun wasu mutane.

Kara karanta wannan

'Babban Abinda Atiku Abubakar Ya Rasa Wanda Ka Iya Jawo Masa Faɗuwa a Zaben 2023'

A yayin da ake wannan zargin, tsohon mataimakin shugaban kasar kawo yanzu bai riga ya yi martani kan zargin da mai tona asirin ya yi ba.

Dan takarar na jam'iyyar PDP zai fuskanci zaben a matsayin daya cikin manyan wadanda ake sa ran za su iya zama shugaban kasa.

APC ta bayyana dalilin da yasa ba a ganin Osinbajo wurin kamfen din APC

A yayin da ake tunkarar babban zaben 2023, jam'iyyar APC mai mulki a kasa ta bayyana dalilin da yasa ba a ganin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wurin kamfen din Bola Tinubu.

Festus Keyamo, mai magana da yawun kwamitin kamfen din takarar shugaban kasa na APC ya ce Shugaba Buhari ne ya ce Osinbajo ya mayar da hankali kan aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164