2023: Tinubu Ya Gana Da Malaman Addini Na Arewa Maso Gabas, Ya Sha Alwashin Kamanta Adalci Da Gaskiya

2023: Tinubu Ya Gana Da Malaman Addini Na Arewa Maso Gabas, Ya Sha Alwashin Kamanta Adalci Da Gaskiya

  • Gabanin babban zaben 2023, an bukaci shugabannin addini su taka muhimmin rawa wurin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a kasa
  • Alhaji Ahmad Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ne ya bada wannan shawarar
  • Ya bayyana cewa ya zama dole shugabannin musulmi su yada koyarwar adalci da gaskiya a tsakanin al'umma

Ɗan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dau alkawarin kamanta adalci tare da bayarda nagartaccen shugabanci idan Allah ya bashi damar zama shugaban Najeriya a 2023.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin zantawa ta musamman da yayi da malamai da shugabannin addinin musulunci da suka fito daga yankin arewa maso gabas da Legit.ng ta samu da Abdulaziz Abdulaziz na ofishin watsa labaran Tinubu ya fitar a ranar Litinin 23 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Ban Ba Yan Najeriya Kunya Ba, Inji Buhari Yayin da Yake Yi Wa Tinubu Kamfen

Bola Tinubu
2023: Tinubu Ya Gana Da Malaman Addini Na Arewa Maso Gabas, Ya Sha Alwashin Kamanta Adalci. Hoto: Tinubu Media Office
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan na Jihar Legas ya ce hakan zai zurfafa hadin kai da samun ribar dimokradiyya tsakanin yan Najeriya a yayin da ake fuskantar zabe.

Jagaban, kamar yadda aka saba kiransa, ya kuma yi kira ga shugabannin addini kada su yi son zuciya amma su yanke hukunci bisa cancanta da ayyukan da yan takarar suka yi.

Yayin taron masu ruwa da tsaki da shugabannin musulunci a Bauchi, Tinubu ya ce:

"Littafin mu na addini ya bukaci mu yi adalci a matsayin masu imani. Allah ya sa mu samu ikon yin hakan.
"Adalci da gaskiya na bukatar a zabi shugabanni bisa la'akari da cancanta, kyawun tunani, halaye da ayyukan da mutum ya yi a baya, a maimakon wasu abu da ba su da alaka da iya jagoranci cikin gaskiya da adalci.
"Tarihi a addinin mu ya nuna yadda manzon tsira ya jagoranci al'umma da ta kunshi masu addinai daban-daban. Bai nuna wata fifiko na musamman ga kabilarsa ko danginsa ba."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Shiga Rudani Yayin da Gangamin APC Ya Zo Karshe Ba Zato Ba Tsammani

Tinubu ya sha alwashin kawo karshen rashin tsaro da ta'addanci

Yayin da ya ke magana da malaman addini a Bauchi, Tinubu ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta cike gurbi tare da ginawa kan ayyukan da gwamnati mai ci yanzu ta ke yi.

Tinubu ya ce:

"Idan aka zabe ni, gwamnati na za ta yi aiki tare da ku, a matsayin malaman addini, don kawo mafita na dindin kan kallubalen da ke tattare da almajiranci."

Wadansu daga cikin malamai kuma shugabannin kungiyoyin addini da suka yi jawabi a wajen taron sun hada da Sheikh Dr. Gambo Kyari, Sheikh Dr. Bashir Sheikh Dahiru Bauchi, Sheikh Salihu Suleiman Ningi da sauransu

Zaben 2023: Yadda zan magance matsalar tsaro idan an zabe ni shugaban kasa, Tinubu ya magantu

Kazalika, dan takarar shugaban kasar APC, ya bayyana wasu cikin muhimman shirinsa ga Najeriya.

Gabanin babban zaben na watan Fabrairu, Tinubu ya ce zai nemi tallafin Kamfanin Gine-Gine na Tarayya don gyara gine-ginen kasar idan an zabe shi shugaban kasa.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Baiwa Yan Najeriya Zabi, Ya Tono Wata Yaudara da Buhari Ya Yi a 2019

Bugu da kari, tsohon gwamnan na Legas ya kuma ce gwamnatinsa za ta yi amfani da dukkan abin da ta ke da shi don magance rashin tsaro.

2023: Arewa ba ta da uzurin rashin zaben Bola Tinubu, Gwamna Ganduje

A wani rahoton, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan Kano ya ce al'ummar arewa ba su da wani uzurin rashin zaben dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu a 2023.

Ganduje ya ce Tinubu ya taka rawar azo a gani wurin ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dare kan mulki, don haka lokaci ya yi da za a masa sakayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel