Yadda APC Ta Yaudari 'Yan Najeriya a Babban Zaben 2019, Atiku

Yadda APC Ta Yaudari 'Yan Najeriya a Babban Zaben 2019, Atiku

  • Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP ya kira APC da sunan jam'iyyar mayaudara
  • Tsohon mataimakin ya tona asirin yadda jam'iyya mai mulki ta yaudari mutanen Neja ana gab da zaben 2019
  • Ya ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yaudari mazauna Neja da ginin tashar jirgin ruwa a Baro

Minna, Niger - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, ya bayyana jam'iyya All Progressive Congress da jam'iyyar mayaudara.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Atiku ya yi bayanin yadda APC mai mulki ta yaudari 'yan Najeriya a babban zaben 2019 domin zarcewa kan madafun iko.

Taron PDP a jihar Neja.
Yadda APC Ta Yaudari 'Yan Najeriya a Babban Zaben 2019, Atiku Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Atiku ya yi wannan furucin ne a wurin ralin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar PDP wanda ya gudana a Minna, babban birnin jihar Neja ranar Asabar.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Zai Iya Kuwa? Bola Tinubu Ya Yi Maganganu Masu Muhimmanci a Jigawa

Ɗan takara a PDP ya ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya cuci mutanen jihar Neja domin ya samu kuri'unsu ya zarce zango na biyu a karagar Mulki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Wani ya zo nan wurin ku cikin hanzari makonni kaɗan gabanin babban zaben 2019 kuma ya kaddamar da fara aikin tashar jirgin ruwan Baro amma tun wancan lokacin ko tsinke ba'a ƙara ginawa ba."
"Kun zaɓe su da tunanin wannan aikin zai yuwu kuma ya jawo ayyukan yi ga musanen ku amma yanzun kun fi kowa sani."

- Atiku Abubakar.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya ƙara da cewa gwamnatin APC ta zo da wani salo 'Canji', a cewarsa sai ga shi canjin ya zo ba yadda mutane suka yi tsammani ba.

Mai neman zama shugaban kasa ya yi alkawarin sake fasalin hanyoyi da tsarin kiwon lafiya idan har ya samu nasara a babban zabe mai zuwa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin Manyan Jihohi 2 da APC Ke Shirin Kwacewa Daga Hannun PDP da Dalili

Zan Kawo Maku Sabuwar Rayuwa inji Bola Tinubu

A wani labarin na daban, Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya ja hankalin mazauna Jigawa su zabe shi

Tinubu ya yi alkawarin sauya rayuwar 'yan Najeriya ta yi kyau idan ya ci zabe shugaban kasa mai zuwa ranar 25 ga watan Fabrairu.

A wurin ralin kamfen APC a Jigawa, tsohon gwamnan ya ɗauki muhimman alkawurran a bangaren ilimi, kiyon lafiya da walwalar jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel