Ban Ba Yan Najeriya Kunya Ba, Na Cika Alkawaran Da Na Daukar Masu, Inji Buhari

Ban Ba Yan Najeriya Kunya Ba, Na Cika Alkawaran Da Na Daukar Masu, Inji Buhari

  • A ranar Litinin, 23 ga watan Janairu ne aka gabatar da gangamin kamfen din shugaban kasa na APC don nemawa Bola Tinubu goyon bayan jama'a
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci tawagar kamfen din zuwa jihar ta arewa inda ya da zango a fadar sarkin Bauchi
  • A jawabinsa, Buhari ya bayyana cewa ya cika alkawaran da ya daukarwa yan Najeriya a yayin zabukan 2015 da 2019

Bauchi - A ranar Litinin, 23 ga watan Janairu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa bai ba yan Najeriya kunya ba a alkawaran da ya daukar masu lokacin zabukan 2015 da 2019.

A yayin da ya kai ziyarar bangirma ga sarkin Bauchi, Dr Rilwanu Adamu bayan ya isa jihar Bauchi don yi wa Tinubu kamfen, Buhari ya ce:

"Ban ba kowa kunya ba."

Kara karanta wannan

Karshen mulki: Saura kwanaki Buhari ya sauka, ya tura sako mai daukar hankali ga 'yan Najeriya

Gangamin APC a Bauchi
Ban Ba Yan Najeriya Kunya Ba, Na Cika Alkawaran Da Na Daukar Masu, Inji Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Yawan jama'ar da suka taru don tarbar Buhari sun ba shi mamaki

Da ya hangi dandazon jama'ar da suka yi masa maraba da zuwa a filin wasa da Abubakar Tafawa Balewa, Buhari ya yi ikirarin cewa hakan ya tabbatar da soyayyar gaskiya da biyayyar da yan Najeriya ke yi masa, rahoton Punch.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin shugaban kasar, Femi Adesina, Buhari ya ce:

"Na kan yi kira ga sarakunan gargajiya da shugabanni, imma yayin yawon siyasa ko na kashin kai zuwa jihohi don nuna godiyata.
"Ina so na ambaci cewa tsakanin 2003 da 2011, na ziyarci dukkanin kananan hukumokin, kuma a 2019, lokacin da nake neman tazarce a karo na biyu, na ziyarci dukkanin jihohin da ke kasar kuma mutanen da suka fito ganina sun zarce wadanda za siya ko a tilasta masu zuwa, na dauki alkawari kuma na sha alwashin cewa zan yi wa Najeriya da yan Najeriya aiki iya karfina kuma zuwa yanzu ban ba kowa kunya ba."

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya saki layin Tinubu? Gaskiya ta fito daga bakinsa, ya bayyana komai

Sarkin Bauchi ya yi jawabi

A nashi jawabin, sarkin Bauchi ya ce abu mai kyau ne yadda shugabannin siyasa suke karrama sarakunan gargajiya da ziyarar bangirma, rahoton Channels TV.

Ya yi godiya ga Shugaba Buhari kan ci gaban da gwamnatinsa ta kawo a jihar Bauchi, yana mai cewa aikin Kolmani ya kafa tarihi wanda jihar Bauchi da arewa maso gabas ba za su taba mantawa da shi ba.

A wani labarin, mun ji cewa daukewar na'urar sauti ya tilasta kawo karshen gangamin APC babu zato ba tsammani a jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel