Dalilin Da Ya Hana Dan Takarar Gwamnan Jihar Kaduna Zuwa Gurin Muhawara

Dalilin Da Ya Hana Dan Takarar Gwamnan Jihar Kaduna Zuwa Gurin Muhawara

  • Dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam'iyyar ADP, Sani Sha'aban bai halarci muhawarar da BBC Hausa ta shirya ba
  • Tunda fari dai a hotan da BBC Hausa ta wallafa yana dauke da hotan yan takara hudu, ciki harda Sha'aban
  • TO sai dai a yau ba'a ga keyar Sha'aban ba a wajen muhawarar a akayi a jami'ar jihar kaduna dake kaduna

Kaduna - An cire dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam'iyyar ADP, Sani Sha'aban daga cikin jerin wanda sukai fafata a muhawarar da shashen Hausa na BBC ya shirya a tsakanin yan takarar gwamna a jihar.

Jam'iyyar ta fadawa mabiyanta da masu goyan bayan dan takarar ta kar su sare, su ci gaba da marawa jam'iyyar baya, kuma Sani Sha'aban na cikin wanda zai fafata da yan takara inji jam'iyyar

Kara karanta wannan

Sabon Matsala Ta Bullo A PDP Yayin Da Buhari Ta Yi Babban Zargi Kan Ayu

Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wajen wani taro da sukai da su, daraktan yakin neman zaben gwamna na jam'iyyar Ben Kure, ya ce an dage gayyatar da aka yiwa dan takarar tasu ne. Rahotan Vangurad

Sha'aban
Dalilin Da Ya Hana Dan Takarar Gwamnan Jihar Kaduna Zuwa Gurin Muhawara Hoto: UCG
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilin da yasa bai halarci muhawarar ba

Jam'iyyar ADP ta ce ta karbi takaradar a ranar 17 ga watan Janairun nan, cewa an cire dan takarar mu daga cikin wanda zasu fafata.

Munyi mamaki da jin wannan batul, sabida yadda muka gani a jikin takaradar shine wai dan takarar gwamna na ADP a jihar Kaduna Jibrin Yusuf ne.

Shin Jibrin yana takara?

Jam'iyyar ADP a jihar Kaduna tace:

"Eh, Jibrin Yusuf ya bi duk wani mataki da ake bi dan zama dan takarar gwamna a jam'iyyarmu, to amma kowacce jam'iyya na neman dan takarar da zai iya kawo kujarer da ya nema dan haka muka dakatar da Jibrin muka sa Sha'aban kuma INEC har yanzu bata dora sunansa ba a shafinta"

Daraktan yakin neman zaben jam'iyyar yace kar wannan ya sanyaya yan jam'iyyar gwuiwa, domin kuwa kwanan nan za'a ga dan takarar ta su na maganganu a kafafen sadarwa na ciki da wajen kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel