Sanatan Da PDP Ta Dakatar Kan Goyon Bayan Tinubu Ya Magantu, Ya Lissafa Kura-Kurai 3 Da PDPn Ta Yi

Sanatan Da PDP Ta Dakatar Kan Goyon Bayan Tinubu Ya Magantu, Ya Lissafa Kura-Kurai 3 Da PDPn Ta Yi

  • Chimaroke Nnamani, sanatan PDP mai wakilitan Enugu East ya yi martani kan dakatar da shi da babban jam'iyyar hamayyar ta yi
  • Nnamani, tsohon gwamnan Enugu, ya bayyana dakatarwar a matsayin rashin adalci don ba a bashi damar kare kansa ba
  • Sanatan ya yi kira ga magoya bayansa su kwantar da hankalinsu a yayin da ake cigaba da kamfen yayin da ya kira dakatarwar a matsayin 'wai'

Enugu - Chimaroke Nnamani, tsohon gwamnan jihar Enugu, ya bayyana dakatar da shi da PDP ta yi a matsayin abin mamaki da daure kai.

PDP ta sanar da dakatar da tsohon gwamnan a daren ranar Juma'a, 20 ga watan Janairu, kan zargin yi wa jam'iyya zagon kasa.

Chimaroke Nnamani
Sanatan Da PDP Ta Dakatar Kan Goyon Bayan Tinubu Ya Magantu, Ya Lissafa Kura-Kurai 3 Da PDPn Ta Yi. Hoto: Chimaroke Nnamani
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Kamfen zub da jini: An sheke wani, da dama sun jikkata a kamfen PDP a wata jihar APC

Nnamani, wanda kuma a yanzu sanata ne mai wakiltan Enugu East a PDP, ya kira dakatarwar da aka masa a matsayin 'wai' a shafinsa na Twitter.

Sanatan ya bayyana kura-kurai uku a dakatar da shi yayin da ya kira magoya bayansa su kwantar da hankulansu a yayin da ake cigaba da kamfen.

Ga hujojjin da ya gabatar

Ba a yi korafi kai na ba

Sanatan ya ce kwamitin ayyuka na kasa, NWC na PDP ba a taba sanar da shi ba ko yin korafi kansa game da dalilin da yasa aka dakatar da shi.

Ba gayyata wurin taro, shari'a ko tattaunawa da NWO

Tsohon gwamnan ya ce NWC na PDP bada taba gayyatarsa ba zuwa wani zama ko shari'a ko bincike kan laifin da ake zarginsa.

Don haka, ya ce ba a bashi damar kare kansa ba, ko ta hanyar tura wakili ko shi da kansa.

Dakatar da shi ya saba kundin tsarin jam'iyya

Kara karanta wannan

Tun yanzu Atiku ya fara yiwa mutane alkawarin kwangila, halin mutum bai canzawa: APC

Don haka, ya kammalawa da cewa dakatar da shi ya saba kundin tsarin jam'iyyar wanda ya ce a bawa mutum damar kare kansa.

A ganinsa, dakatarwar da aka ce an yi masa ba a bi tsarin ladabtarwa ba don haka ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ga rubutunsa a kasa:

Jam'iyyar PDP ta dakatar da Sanata Chimaroke Nnamani da ke goyon bayan Tinubu

Tunda farko, kun ji cewa babban jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta dakatar da Chimaroke Nnamani, sanata mai wakiltar Enugu East a majalisa.

Mai magana da yawun jam'iyyar PDP na kasa, Debo Ologunaba ne ya bayyana hakan cikin wata takarda da ya fitar.

Ya ce ana zargin Nnamani da cin amanar jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel