Jam’iyyar PDP ta Dakatar da Sanatan Da Ke wa Tinubu Kamfen

Jam’iyyar PDP ta Dakatar da Sanatan Da Ke wa Tinubu Kamfen

  • Jam'iyyar PDP ta dakatar da Sanata Chimaroke Nnamani mai wakiltar mazabar Enugu ta yamma a majalisar dattawa daga jam'iyyar
  • Ba Nnamani kadai ba, jam'iyyar ta dakatar da wasu karin mutum bakwai da ta ke zargi da lamurran zagon kasa ga jam'iyyar
  • Jam'iyyar tayi kira ga shugabanni, masu ruwa da tsaki da sauran 'yan jam'iyyar da su mayar da hankali wurin cetowa tare da gina kasar nan

FCT, Abuja - Jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP, ta dakatar da Chimaroke Nnamani, sanata mai wakiltar mazabar Enugu ta yamma a majalisar dattawa.

Labari da dumi
Jam’iyyar PDP ta Dakatar da Sanatan Da Ke wa Tinubu Kamfen
Asali: Original

Debo Ologunagba, kakakin jam’iyyar PDP ya sanar da wannan cigaban a takardar da ya fitar a daren Juma’a, jaridar TheCable ta rahoto.

Yace Nnamani da wasu mutum bakwai aka dakatar kan lamurran zagon kasa ga jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tagwayen Abubuwa Masu Fashewa Sun Tashi a Wurin Kamfen din APC a Fatakwal, 3 Sun Jigata

Ologunagba yace wannan hukuncin an yanke shi ne bayan an yi bita sosai kan lamurran jam'iyyar a kasar nan dogaro da kundin tsarin PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya lissafa mutum bakwa da dakatarwan ta hada da su kamar haka: Ayeni Funso Ekiti ta arewa, Ajijola Lateef Oladimeji (Ekiti ta tsakiya), Emiola Adenike Jennifer (Ekiti ta kudu II), Ajayi Babatunde Samuel (Ekiti ta arewa II), Olayinka James Olalere (Ekiti ta tsakiya), Akerele Oluyinka (Ekiti ta arewa I), da Fayose Oluwajomiloju John (Ekiti ta tsakiya I).

Jam'iyyar PDP tace dakatarwan tasu za ta fara amfani a take.

"Kwamitin aiwatar da ayyuka na jam'iyyar PDP na kasa bayan bita da duba lamurran jam'iyyarmu a kasar nan, dogaro da tanadin kundin tsarin PDP da aka gyara na 2017, ya amince da dakatar da Sanata Chimaroke Nnamani na jihar Enugu da Cif Chris Ogbu na jihar Imo daga yau, Juma'a, 20 ga watan Janairun 2023 kan zargin zagon kasa da jam'iyyar."

Kara karanta wannan

Babban Mai Daukar Nauyin APC da Dubban Mabiyansa Sun Bar Tafiyar Tinubu, Sun Koma PDP

- Takardar tace.

"Jam'iyyar PDP tayi kira ga dukkan shugabanninta, masu ruwa da tsaki da mambobin jam'iyyar na fadin kasar nan da su kasance masu hadin kai da mayar da hankali kan burin jam'iyyar na ceto, sake gina da tsara kasar nan a shugabanci."

- Ya cigaba da cewa.

Duk da zamansa mamban jam'iyyar PDP, Nnamani a bayyana ya ke bayyana goyon bayansa ga Bola Tinubu, 'dan takarar jam'iyyar APc na shugabancin kasa.

A watan Disamban 2022, tsohon gwamnan Enugun yace yana goyon bayan Tinubu ne duba da burin yankin kudu maso gabas.

"Ba neman mukamin minista na ke ba sabida na wuce wannan wurin. Muna yin wannan ne saboda abinda mutanenmu ke so."

- Yace.

Sanata Nnamani ya magantu bayan ganin sunansa a tawagar kamfen din Tinubu

A wani labari na daban, Sanata Chimaroke Nnamani ya bayyana dalilin da yasa sunansa ya bayyana a cikin tawagar kamfen din Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima.

Ya sanar da cewa yana cikin magoya bayan Tinubun saboda ya san nagartar da ya nuna yayin da yayi gwamnan jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel